1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceGabas ta Tsakiya

Mece ce makomar mazauna Zirin Gaza?

Mahmud Yaya Azare LMJ
August 20, 2025

Kwana guda bayan Hamas ta shelanta amincewarta da daftarin yarjejeniyar kawo karshen yaki a Gaza da sakin illahirin wadanda take garkuwa da su, Isra'ila ta mai da martani da shelanta fara aiwatar da shirin mamaye Zirin.

Isra'la | Israel Katz | Mamaya | Zirin Gaza | Falasdinu
Ministan tsaron Isra'ila Israel KatzHoto: Hannes P Albert/dpa/picture alliance

Ministan tsaron Isra'ilan Israel Katz ne ya sanar da hakan ga dandazon sojoji, alokacin da yake ziyara a barikin soja na birnin Haifa. A cewarsa har yanzu tsugune ba ta kare wa dakarun sojojin na Isra'ila da ke yaki da abun da ya siffanta shi da bakin ta'addacin Hamas ba. Ministan ya sanar da shirin samar da tuddan tsira a cikin kwaryar Zirin na Gaza da zaratan mayakan Falasdinawa masu dauke da makamai ke jan daga, domin bai wa fararen hula kariya. Kafin hakan dai, firaminista Isra'ila Benjamin Natenyahu ya samu sahalewa daga majalisar dokoki kan mamaye illahirin Zirin Gaza, domin ya zama wani jigo na dorewar tsaron Tel Aviv.

Tuni dai kungiyar Hamas ta yi tir da sabon nhirin mamayar, tana mai jaddada aniyarta ta ci gaba da yin fito na fito kamar yadda shugaban kungiyar ta Hamas a ketare Usama Hamdan ya nunar. A nata bangarena, kasar Masar da ke makwabtaka da Zirin Gaza a iyakarta da jihar Sinai, ta sanar da jibge dakarun sojanta dubu 40 a iyakarta da Gaza domin kandagarkin abun da zai kai ya komo. A watan da ya gabata dai, shugaban Masar Abdulfattah al-Sisi ya siffanta yunkurin Isra'ila na korar Falasdinawan Gaza zuwa cikin kasarsa da wani jan layi da keta shi zai kawo karshen yarjejeniyar zaman lafiyar da suka cimma da Isra'ila tun shekarar 1975 bayan yakin kare jini biri jinin da kasashen biyu suka gwabza da har Masar din ta 'yanta yankunanta da Isra'ila ta mamaye a shekarar 1967.