Nijar: Ko har yanzu ana damawa da mata?
May 13, 2026
Wannan rana ta 13 ga watan Mayu shekarar bana ta 2026 dai, na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke cikin wata sabuwar tafiyar juyin-juya hali. Bayan juyin mulkin sojoji, maatan kasar na da ga cikin na kan gaaba wajen marawa mulkin sojan baya. Matan dai sun yi ta yin tarukan gaangami, tun lokacin da kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO ta kakabawa Nijar din takunkumi sakamakon juyin mulkin. Sun ma yi zaman dirshan a birnin Yamai, domin nuna adawarsu da kaasancewar sojojin kasashen ketare a kasar.
Da dama dai daga cikin matan sun rabauta da mukamai a gwamnatin mulkin sojan, ganin irin jajircewar da suka yi a wannan sabuwar tafiyar. Wasu dai na kallon matakin ba su mukamman, a matsayin wani ladan aikin da suka yi. To saidai kuma mata a yankin Agadez na ci gaba da korafin rashin damawa da su musamman a zauren wakilai na majalisar tuntubar juna, inda babu mace daya tilo a cikin tsarin sabanin sauran yankunan kasar.
Gyarawa da wallafawa: Lateefa Mustapha Ja'afar