Jamhuriyar Nijar: Ina makomar ilimi?
June 3, 2025
Cikin wata sanarwar da babbar kungiyar dalibai ta kasa ta Nijar din ta fitar, ta ce yanayin da aka shiga na kafewa kan baka ba tare da fuskantar juna domin nazarin matsalolin ba na saka tsarin karatu cikin halin rashin tabbas musamman ma a wannan lokaci da ake shirin fara jarabarawar karshen shekara. A dangane da haka ne kungiyar ta USN ta yi kira ga ofishin ministan ilimi da horo na kasa da ya dubi girman wannan matsala, domin samar da kyakkyawar mafita. Cikin sanarwar kungiyar daliban ta yi tir da yanayin da aka shiga, inda makarantun gwamnati kusan suka tsaya cak yayin da masu zaman kansu ke aiki.
Tuni dai shugabannin kungiyar iyayen 'yan makaranta suka ce suna ciki tattaunawa da bangarorin, domin samun mafita. Sai dai Honorable Alhaji Mouazou Tchagalla tsohon dan majalisar dokoki kuma uba ya ce, batun ilimi na yara wanda sune manyan gobe wajibi ne kuma bai kamata a yi ja-in-ja a kani ba. An dai jima ana fama kan wanan batu na magance matsalar kwantaragi a fannin ayyukan malaman makaranta a Nijar, inda aka sha zama tsakanin gwamnati da kungiyoyin malaman domin samun jituwa a fannin daukar malamai a matsayin ma'aikatan din-din-din.
Acewar Kassoum Issa tsohon magatakarda na babbar kungiyar Malaman Makaranta ta kasa, lokaci ya yi da ya kamata a dauki matakan gyara. Kungiyar dalibai da 'yan makaranta na kasa baki daya dai ta yi kira ga magoya bayanta 'yan makaranta da su hada kai, domin ganin sun fuskanci wannan matsala da kuma kwato hakkokinsu na samun karatu yadda za su samu kyakkyawar makoma.