1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

NATO: Ko Jamus za ta iya jagorantar Turai?

July 9, 2024

A wannan mako kungiyar Tsaro ta NATO ke gudanar da babban taronta a birin Washington na Amurka, a daidai lokacin da take cika shekaru 75 da kafuwa.

Amurka | Washington | Taro | NATO | Shekaru 75 | Jamus | Turai
Taron kungiyar Tsaro ta NATO, a daidai lokacin da ta cika shekaru 75 da kafuwaHoto: Noah Berger/AP Photo/picture alliance

Baya ga batun yakin Rasha da Ukraine da ke daukar hankalin taron kungiyar ta NATO, akwai kuma fargabar abun da ka iya ka iya faruwa idan har Donald Trump ya yi nasarar sake darewa kan karagar mulkin Amurka a babban zaben kasar da ke tafe a watan Nuwamba. Jamus dai na zaman kasa ta biyu bayan Amurka, wajen a bayar da kudin tallafi ga Ukraine. Hukumomin Berlin sun ware makudan kudi kudi na musamman da yawansu ya kai Euro biliyan 100 kan batun da ya shafi tsaro, kana a bana kasar ta cimma tsarin NATO na biyan kaso biyu cikin 100 na yawan kudin shiga daga kayayyakin da ake kerawa a cikin gida. Firaministan kasar Poland Donald Tusk ya fito a karara ya bayyana cewa kasashe mambin NATO daga Turai na kara dora tsammaninsu kan  Jamus, domin ta samar musu tsaro.

Batun karin tallafi ga Ukraine, ka iya zama babban abin da taron zai mayar da hankaliHoto: DW

A karon farko Jamus din za tura bataliyar sojoji zuwa kasar Lithuaniya, domin su taimaka wajen tsare iyakar NATO da Rasha daga gabashi. Kuma shi kansa shugaban gwamnatin Jamus din Olaf Scholz ya jaddada cewa, batun tsaro shi ne kan gaba a manufofin Berlin. Sai dai a cewar ministan tsaron Jamus Boris Pistorius duk da wannan kalaman da ake ji kan tsaro daga bakin gwamnatin kasar, kudin da aka ware a kan batun tsaro a kasafin bana ya gaza da Euro biliyan shida da abin da suka nema tun da farko. Amma Scholz ya kara jaddada cewa koda a ba samu kudin da ake bukata ba a kasafin kudin, nan da shekaru uku Jamus za ta ci gaba da bayar da adadin da tsarin NATO ya kayyade. Babbar matsalar da Jamus ke fuskanta wajen jagoranci a kungiyar NATO shi ne kayan yakin Rundunar sojojin karar duk tsofaffi ne, kuma babu wani kudi za a iya fitar wa da za su sabunta makaman yakin cikin karamin lokaci. Yayin da a hannu guda Amurka ke son ta mika nauyin kula da kungiyar NATO ga wata kasa a Turai, akwai bukatar Jamus ta fitar da kudin da ake da bukata a fannin tsaron domin kare makomar Turai.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani