1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Rasha: Maka EU a kotu ne mafita?

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 12, 2025

A nan kuma babban bankin Rasha ya maka kamfanin Euroclear a kotu, a wani mataki na mayar da martani kan matakin da kungiyar Tarayyar Turai EU, ke shirin dauka na rike kudin Moscow da ke kasashen EU din har abada.

Belgium | Brussel | Euroclear | Rasha
Kamfanin Euroclear da ke tantance hada-hadar kudi a TuraiHoto: Werner Lerooy/Imago

Kamfanin na Euroclear da ke da shalkwata a Brussels babban birnin kasar Belgium ne dai, ke juya akalar kimanin euro biliyan 185 cikin euro biliyan 210 da kasashen Tarayyar Turan EU suka rike na Rashan, sakamakon yakin da take da makwabciyarta Ukraine. A yanzu dai wannan kudin na Moscow na karkashin wani tsari ne na takunkumi da kasashen EU din suka dauka, wanda suke sabunta shi duk bayan watanni shida, domin samun damar ci gaba da rike su.