1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Fara sabuwar hulda da kasashen waje

Salissou Boukari LMJ
January 16, 2026

Wasu sababbin jakadun kasashe takwas, sun gana da shugaban gwamnatin mulkin soja ta Jamhuriyar Nijar Janar Abdourahamane Tiani, Daga cikin jakadun akwai na Rasha Thailand.

Jamhuriyar Nijar | Shugaban Kasa | Mulkin Soja |  Janar Abdourahamane Tiani
Jagoran gwamnatin mulkin soja ta Jamhuriyar Nijar Janar Abdourahamane TianiHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

Jakadun dai sun hada da na Mauritaniya da Jamus da Rasha da Ingila da Indonesiya da Thailande da Portugal da Austriya, wanda wasunsu ke da zama a wasu kasashe kamar Najeriya da ma jakadan Ausrtiya da ke da zama a Algeriya da na Somaliya da ke a Sudan ta Kudu. Abin lura ne cewa a karon farko ne kuma a tarihinta, Nijar ta karbi bakuncin jakada mai cikakken iko na masarautar Thailand.

Farfado da huldar diplomasiyya?

Batu na biyu da ya ja hankali shi ne na samun jakadan Rasha da mazauna a nan birnin Yamai, sabanin shekarun baya da babu irin wannan hulda. Bisa dokokin kasa da kasa da tsari na diflomasiyya, karbar wadannan jakadu da shugaban kasar Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya yi, na nuni da cewa ya amince da wadannan manyan wakilai a hukumance. Matakin kuma na nuni da farkon kama aikinsu na diflomasiyya, domin karfafa dangantaka a tsakanin kasashensu da Nijar.

Abubuwa Biyar tare da Sedik Abba

04:20

This browser does not support the video element.

Ana kuma kallon matakin a matsayin wata dama ta buda tattaunawa da karfafa aminci da sauran al'ummomin wadannan kasashe na Turai da Asiya da Afrika da kuma Rasha. Farfesa Dicko Abdourahamane Malami a jami'ar birnin Damagaram kuma masanin siyasar kasa da kasa ya nunar da cewa: "Kasancewar jakadan Rasha a zaune a nan Nijar, ba karamin ci-gaba ba ne idan aka la'akari da tafiyar siyasar duniya a yanzu."

Koma wa tafarkin dimukuradiyya ne mafita

Sai dai ga masu adawa da gwamnatin ta mulkin soja da fatan ganin an koma kan cikakken tafarki na dimukuradiyya kamar Tahirou Garka mai Magana da yawun kungiyar adawa ta G25, ba suga wani tasiri da huldar Rasha da Nijar za ta yi ga al'ummar kasar ta Nijar ba. Masu lura da al'amura na diflomasiyya a kasar ta Nijar dai na ganin duk kasar da ta amince ta yi hulda da Nijar a yanzu, za ta amince ne kan sabon matakin kasar ta Nijar na kasancewa kasa mai cikakken 'yanci.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani