1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ko rikicin PDP ya kawo karshe?

Ubale Musa/LMJJuly 27, 2016

Bayan share tsawon lokaci cikin rikici dai, akwai alamun lamura na neman komawa dai-dai a cikin jami'yyar PDP mai adawa a Najeriya da ta share lokaci ta na fama da rikici na cikin gida.

Jam'iyyar PDP na kokarin sasanta rikicin cikin gida
Jam'iyyar PDP na kokarin sasanta rikicin cikin gidaHoto: DW/K. Gänsler

Alamun komawa dai-dai din sun faro ne tare da wani babban taron jam'iyyar makonni kusan ukun da suka shude in da bangaren na Ahmed Makarfi ya amince da ranar 17 ga watan Augusta mai zuwa domin babban taro na kasa a Fatakwal. Tun bayan nan dai alamun motsin ran jam'iyyar ta PDP ya fara nunawa tare da kai wa ga amincewa da Makarfin a bangaren hukumar zaben kasar ta INEC a cikin wannan mako. Ya zuwa yanzu dai tuni jam‘iyyar tai nasarar rabon Mukamai 22 da ake shirin fafatawa a wajen taron na Fatakwal a tsakanin sashen Arewacin kasar da dan uwansa da ke Kudu. Daga dukkan alamu dai jiga-jigan 'yan PDP sun yi nasarar mantawa da batun rikici tare da mai da hankali ya zuwa taron na Fatakwal, da jam'iyyar ke fatan zai zamo dan bar kai wa ga sake haihuwar jam'iyyar, kuma tuni a fadar Aminu Wali da ke zaman daya a cikin 'ya'yan da suka kai ga kyankyasar PDP tun daga fari, wai sun dau darasi mai zafi kuma sun shirya sake tasiri a cikin fagen siyasa na kasar.

Da na sani da karatun ta nutsu

Da na sanin karatun baya ko kuma neman hanyar gina tubali na gaskiya da amana dai, babban burin 'ya'yan PDP dai na zaman hada karfi wuri guda da nufin karbe mulki a cikin kankani na lokaci daga hannun 'yan sauyin da suke fafutukar nemo hanyar warware matsaloli na kasar. Abun kuma da a cewar Sule Lamido da ke zaman tsohon gwamna na Jigawa bai wuci cire riga a wuyan yaro ba.

Cikin 'yan lemar kyankyasa ta tsintsiya dai, duk da hadewar jam'iyyar wuri guda jan aikin da ke tsakanin PDP da bude sabon babi na zaman makoma ta Ali Modu Sharrif da har yanzu yake ta jan kafa yana ikirarin zama halastaccen shugaba ga jam'iyyar. Tuni dai bangaren na Sherrif ya nisanta kansa da taron na Fatakwal, sannan kuma ya nemi sauka ta Makarfin tare da hada wani kwamitin sulhu da zai jagoranci harkokin jam'iyyar zuwa ga babban taron.

Tsohon shugaban Najeriya karkashin jam'iyyar PDP Goodluck JonathanHoto: picture-alliance/AP

Makomar Ali Modu Sheriff a PDP

A yayin da jiga-jigan PDP na Arewacin kasar ke taron tsarin mafita ta gaba, Sherrif din ya share wuni guda a birnin Enugu yana ta Owambe da kawaye. Babban karfi na Sherrif din na kara karkata ga kotunan kasar, maimakon 'ya'yan lemar da kusan dukkaninsu ke nuna alamun kware masa baya yanzu. Abun kuma da a cewar Shehu Musa Gabam da ke zaman jigon jam'iyyar daga sashen Arewa maso Gabas ta Sharrif din, ya sanya sauyi na tunani zama na wajibi a gareshi. Abun jira a gani dai na zaman iya kai wa ga tudun mun tsira ga jam'iyyar da ke da jan aiki na adawa, amma ta share lokaci tana fada a tsakanin 'ya'yanta.