Najeriya: Ko sabuwar jam'iyyar ADC za ta dore?
July 8, 2025
Duk da cewar dai a cikin biki da babban buri ne aka kai sake haihuwar ADC, tun ba ta kai ga fara rarrafe ba ga dukkan alamu tana shirin fuskantar kalubale irin na manyan 'ya'ya a cikin gidan na siyasa. Wasu da suka kira kansu shugabanni a unguwannin jihohin Nasarawa da kuma Kogi, sun shigar da kara a gaban wata kotun da ke Abuja, suna neman haramta shugabancin jam'iyyar ADC a karkashin David Mark. Jami'an uku da suka ce suna wakiltar wasu 'yan jam'iyyar 30 dai sun ce, shugaban jam'iyyar ba shi da ikon mika ragamar harkokinta ba tare da amincewar majalisar zartarwar jam'iyyar ba.
Karin Bayani: Najeriya: Ko 'yan adawa za su yi nasara a 2027?
Duk da cewar dai kotun da ke zamanta a Abuja fadar gwamnatin kasar ba ta saka ranar fara sauraron shari'ar ba, ana kallon isa gidan alkalan da kokarin tsomin bakin APC 'yar mulki. Masu tsintsiyar dai, ba su boye kokarin tabbatar da haramcin sabon auren da ke ta yamutse hazo cikin gidan na siyasa ba. Salo na kokarin raba kai ne dai ake zargin jam'iyyar APC mai mulki da bi, wajen raba kai cikin gidan na adawa. Salon kuma da ya kalli rigingimu a zauren kotu, a kusan dukkanin jam'iyyun da ke batun adawa a cikin Tarayyar Najeriyar. Kuma a cewar Solomon Dalung da ke zaman jigo a cikin ADC, ba zai aike tsoro cikin gidan na adawa ba.
Abdullahi Tanko dai na bai wa shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu shawara a harkokin al'umma, kuma ya ce ADC ta bullo a duniya babu uba. Koma ya take shirin da ta kaya cikin gidan alkalan a tsakanin masu korafin ba daidai da masu tangadin kama-karya, shari'ar dai na nuna alamun jan aikin da ke gaban ADC a kokari na karbar mulkin. Tun kafin ADC dai da ma su ma yayyenta can cikin gidan na adawa, har yanzu na ta kokarin kwance daurin gwarman da ake zargin APC da yi da sunan shari'a. Kama daga PDP ya zuwa SDP da ma jam'iyyar Labour dai, kusan dukkanin masu takama da adawa na kiki-kakar neman tabbatar da shugabancin daidai cikin gidan alkalan a yayin kuma da ake kara kusantar zabukan da ke da tasiri ga rayuwa da makoma.
Karin Bayani: Ina makomar jam'iyya mai mulki a Najeriya?
To sai dai kuma rikicin gidan ADC a tunanin Barrister Buhari Yusuf da ke zaman wani lauya mai zaman kansa a Najeriyar, har yanzu bai nuna alamun hayaki ba balle a tsammaci gobarar da ke iya dauka ta hankali cikin gidan na siyasa. Duk da cewar dai masu karar ba su da tasirin da ke iya kaiwa ga tada hankali a tarukan jam'iyyar, goyon baya na masu tsintsiyar na iya kaiwa ga tayar da hargitsi mai girma cikin gidan ADC, ya zuwa yanzun dai sabuwar jam'iyyar na ta kakkaba daga 'ya'yan jam'iyyu na adawa da ke mafi yawa na sassa na arewacin kasar.