Najeriya: Ko sarakuna na da rawar takawa?
October 31, 2024Wani juyin mulkin soja ne dai, ya kare rawar sarakuna cikin lamuran mulkin Tarayyar Najeriya daga jamhuriya ta farkon fari. To sai dai kuma rikicin rashin tsaro da karuwa ta talauci, na neman sake mai da su bisa taswirar tafi da Najeriyar. Masu mulki na kasar sun ayyana sake samar da rawar takawa, ga dubban sarakunan gargajiyar. Wani taro da ke zaman na farko a tsakanin sarakuna da gwamnoni na kasar dai, ya kare tare da yanke shawarar kafa wani kwamiti da zai jagoranci sake bai wa sarakunan murya a cikin harkokin tafiyar da kasa. Gwamnonin dai, sun ce suna shirin goyon bayan damar taka rawar sarakunan cikin gyaran kundin tsarin mulkin da ke gaban majalisun Najeriyar biyu. Sabuwar dabarar 'yan mulkin dai na kara fito da irin jan aikin da ke gaban kasar fili, inda ta kai ga kisan kudi maras adadi amma kuma ta kasa kai wa ya zuwa zaman lafiya. To sai dai kuma babban kalubalen da ke gaban sarakunan, na zaman iya kawo sauyin da ya kai ga gagarar kundila cikin kasar. Kai wa ya zuwa zaman lafiya cikin tsohon tsari ko kuma alamu na kara rudewar lamura, duk da cewar dai sarakunan Najeriyar na nuna alamu na tsintsiya madaurinki daya.