1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTanzaniya

Tanzaniya: Ko Shugaba Samia za ta zarce?

Cai Nebe AMA/LMJ
October 22, 2025

Yayin da ya rage mako guda a gudanar da babban zaben kasar Tanzaniya da Shugaba Samia Suluhu Hassan ke hankoron neman tazarce, kallo ya koma kan yadda za ta kasance a rumfunan zabe ranar 29 ga wannan wata na Oktoba.

Tanzaniya | Zabe | Shugaban Kasa | Samia Suluhu Hassan
Shugaba Samia Suluhu Hassan na shirin yin tazarce a TanzaniyaHoto: CCM

Kundin tsarin mulkin Tanzaniya ya yi tanadin zabar shugaban kasa tare da mataimaki da za su yi shekaru biyar a zangon farko na mulki, tare da damar sake neman zango na biyu kuma na karshe ga duk wanda ya taba shugabantar kasar. Ko da yake wannan ne karon  farko da Shugaba Samia Hassan ke shiga takarar shugaban kasa, kasancewar ta maye gurbin marigayi Shugaba John Magufuli da ya rasu a shekarar 2021 ne.

Ta ya aka samar da Tanzaniya?

A shekarar 1964 Tsibirin Zanzibar ya hade da yankin Tanganyika, domin zama kasar Tanzaniya mai mutane miliyan 68. To amma al'ummar Zanzibar ba su haura miliyan biyu ba, wadanda kashi 98 cikin 100 ke bin tafarkin addinin Musulumci. A jimlace dai, kaso 63 cikin 100 na al'ummar kasar Kiristoci ne.

Bibi Titi Mohamed: "Uwar kasa" ta Tanzaniya

01:58

This browser does not support the video element.

Majalisar dokokin Tanzaniya ta kunshi mambobi 264, wato 214 daga Tanganyika sai 50 daga Zanzibar. Wani abin misali shi ne, tagomashin da mata ke da shi a kundin tsarin mulkin kasar da ya ware kujeru 113 ga mata kadai. A wannan zabe na ranar 29 ga wannan wata na Oktobar, 'yan takara 17 ne ke da muradin darewa kan karagar shugabancin Tanzania.

Karin Bayani: Mecece makomar 'yan adawa a Tanzaniya?

Sai dai kuma hankali ya fi karkata kan Shugaba Samia Suluhu Hassan ta jam'iyyar Chama Cha Mapinduzi wato CCM, sakamakon yadda hukumomin kasar suka haramtawa manyan jiga-jigan adawa tsayawa takara. Daga cikinsu har da Tundu Lissu na jam'iyyar Chadema da ke fuskantar tuhumar cin amanar kasa, bayan da ya bukaci a sauya kundin zaben kasar. Akwai kuma Othman Masoud Othman na jam'iyyar Alliance for Change and Tranparency, wanda aka fi sani da Wazalendo.

Tanzaniya da ta ninka kasar Jamus sau uku na da ingantattun tituna masu nagarta da suka karade dukkan sassanta, baya ga ingantaccen tsarin wutar lantarki da layin dogo da kuma intanet. Ko da yake akwai bukatar kara himma daga mahukunta wajen habaka fannin ilimi da samar da ayyukan yi, wadanda na daga cikin korafe-korafen da masu zaben ke fatan ganin an kyautata.

Jam'iyya daya tilo?

Julius Nyerere: Jagoran samun 'yanci

01:31

This browser does not support the video element.

Jam'iyyar CCM ta Shugaba Samia Hassan ce ke jagorantar kasar tun bayan samun 'yancin kaidaga Turawan Mulkin Mallaka na Birtaniya a shekarar 1960, bayan damka mulkin a hannun shugabanta na farko marigayi Julius Nyerere. Ta yi wu, wannan na daga cikin dalilan da ke sanya 'yan kasar bukatar samun sauyin hannu daga masu jan akalar tasu.

Ko Samia Hassan za ta iya tsallake wannan siradi? Da dama sun nuna farin ciki lokacin da ta dare madafun iko a shekarar 2021, la'akari da gashin kumar da 'yan adawa da kafafen yada labarai suka sha a hannun magabacinta marigayi Magafuli.

To sai dai jim kadan da kammala daidaita zamanta a kan karaga, sai ta dora daga inda ya tsaya wajen muzgunawa 'yan adawa da sauran 'yan gwagwarmaya. Daga nan ne kuma, mulkinta ya shiga shan suka daga bangarori dabam-dabam. Yanzu dai kowa ya wasa wukarsa a kasar ya kasa ya tsare, dominn ganin yadda za ta wanye a lokacin zabe.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani