1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Merz ya bukaci Trump ya takawa Rasha birki

Lateefa Mustapha Ja'afar
June 5, 2025

Shugaban Amurka Donald Trump ya sake yin kememe wajen fitowa fili ya soki Rasha kai tsaye, dangane da yakin da ta kwashe sama da shekaru uku tana fafatawa da makwabciyarta Ukraine.

Amurka | Washington D.C. | 2025 | Donald Trump | Jamus | Friedrich Merz | Ganawa
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz da shugaban Amurka Donald TrumpHoto: Evan Vucci/AP/picture alliance

Sabanin babban bakonsa shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz da ya dora laifin gaza cimma matsayar tsagaita wuta kacokam a kan Moscow da ayyana Rashan a matsayin babbar azzaluma, ko da aka tambaye shi ko zai dauki tsattsauran mataki a kan Rashan Trump ya ce zai dakata har zuwa lokacin da yakin yaki tsayawa kafin ya nuna wa Rasha kurenta.

Ya kuma kara da cewa kasashen biyu ne ya kamata su nuna aniyarsu ta dakatar da yakin, yana mai cewa tamkar yara biyu ne suna fada a filin wasa a wasu lokutan gara a kyale su sai su kece raini. Merz dai ya ce ya bayyanawa Trump karara cewa shi yake da damar taka wa Moscow birki, ya kuma jaddada aniyar sake tattauna batun yayin da za su yi ganawar keke da keke shi da Trump din.