1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIran

Iran: Ko tsarin juyin-juya hali zai dore?

Mahmud Yaya Azare LMJ
February 11, 2026

Ana gudanar da bukukuwan cika shekaru 47 da juyin-juya halin Musulunci da aka yi a kasar Iran ne a bana, a daidai lokacin da tsarin Jamhuriyar Musuluncin ke fuskantar wani gagarimin kalubalen d ba a taba ganin irinsa ba.

Iran | Juyin-juya Hali | Musulunci | Kalubale | Zanga-zanga | Tattalin Arziki | Tsadar Rayuwa
Dubun-dubatar mutane, sun halarci bikin tunawa da juyin-juya halin Musulunci a IranHoto: Majid Asgaripour/WANA/REUTERS

Wasu na hasashen akwai barazana ga dorewar tsarin juyin-juya halin a kasar ta Iran, ballantana ma yada shi ko tallata shi a kasashen ketare. A yanzu dai Iran ba kawai tana yaki da takunkuman kasashen waje ba ne, tana kuma fuskantar wutar boren cikin gida wacce ke neman girgiza harsashin juyin-juya halin.

Raunin tattalin arziki

Babban kalubalen farko shi ne rugujewar tattalin arziki, inda hauhawar farashin kaya ya kai sama da kaso 40 cikin 100. Farashin kayan abinci na yau da kullun ya ninka har sau biyu, a cikin watanni shida kacal. Kudin kasar wato Rial, ya rasa kusan dukkan darajarsa a kasuwannin duniya. Wannan ya jefa miliyoyin 'yan kasar cikin kangin talauci, wanda ya sa talakan Iran yake ganin cewa manufofin juyin-juya halin ba sa amfana masa ta fuskar rayuwa. Karancin hasken wutar lantarki da man fetur a kasar da ke sahun gaba wajen albarkatun mai, ya zama abin kunya ga gwamnatin Tehran.

Bore a cikin gida
Matsin tattalin arziki ya haifar da gagarumar zanga-zanga, tun daga karshen shekarar 2025. Ba kamar zanga-zangar baya ba, wannan boren ya mamaye dukkan larduna 31 na kasar. Masu boren da mafi yawansu matasa ne, ba gyara kawai suke nema ba suna bukatar sauyi ne. Katse Internet da gwamnati ta yi tun ranar takwas ga Janairun 2026, ya rage yaduwar bidiyo zuwa duniya. Amma bai kashe muryar da ke tashi daga unguwannin Tehran da Isfahan ba, kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun ce akwai dubban mutanen da aka tsare ko aka kashe a wannan takun-saka.

An yi asarar dukiya da rayuka masu yawa, a yayin zanga-zangar tsadar rayuwa a IranHoto: IRIB/WANA/REUTERS

Wariya a fannin diplomasiyya

Bayan kazamin rikici da Isra'ila a shekarar 2025, dakarun kare juyin-juya hali na IRGC na fuskantar sababbin matsin lamba. Kasashen Turai da Amurka sun kara kaimi wajen kakkaba takunkumi, yayin da kungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran a yankin Gabas ta Tsakiya ke kara raunata. Wannan ya bar Iran tana fuskantar barazana kai tsaye ga cibiyoyinta na nukiliya da na tsaro, ba tare da kariya mai karfi daga kawayenta ba.

Karya lagonta a ketare.

Bayan rubdugun da Isra'ila da Amurka sukai wa kungiyoyi 'yan barandan Iran a ketare da suka hada da Hezbollah ta Lebano da Hamas a Gaza da 'yan Huthi a Yemen da ma mayakan sa-kai a Iraki, a iya cewa an sare kumbar da kasar ta Iran ke amfani da ita wajen yagunin abokan hamayyarta da ma tallata akidar juyin-juya halin Musuluncin a ketare. A yanzu, jagororin juyin-juya halin da kasar ta Iran ns ta kansu.

Makomar shugabanci

Daga karshe, akwai tambayar da kowa ke tsoron amsawa: Mene ne zai faru, bayan jagoranci na yanzu? Takun-saka tsakanin masu ra'ayin mazan jiya da masu son sassauci a cikin gwamnati, ya haifar da rashin tabbas kan wanda zai karbi ragamar juyin-juya halin. Wannan rarrabuwar kawuna a cikin gida, na iya zama babban hadari fiye da kowane takunkumi na waje. Juyin-juya halin Iran, na cika halin tsaka mai wuya da ke bukatar gudanar da gagarumin sauyin da zai hada tsakanin manufofinsa na asali da bukatun yau da kullum na 'yan kasa.

Haka kuma a mutumta burace-buracen matasa da mata da sune galin 'yan kasar, kamar yadda yake bukatar kwararaun jami'an diplomasiya da suka iya kauciya da zamiya da kuma ke da sassauci a lokacin da ya kama, domin kaucewa igiyar tekun da ke kokarin yin awon gaba da tsarin Jamhuriyar Musuluncin Iran din.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani