Kenya: Ko 'yan majalisa na karbar cin-hanci?
August 28, 2025
Shugaba William Ruto ya yi wannan zargi da ya yamutsa hazo a taron hadin gwiwa na majalisun dokokin Kenya, ranar 18 ga watan nan na Agusta. Wasu na zargin wannan wani kokari ne, na kawar da hankalin 'yan kasa daga alkawuran da ya gaza cika musu tun lokacin yakin neman zabe. A cewar Shugaba Ruto ya ce wannan halayya da ta zama jiki a tsakanin masu yin doka ta bibiyar mutane suna karbe musu kudi ta zubar da kimar majalisar, a don haka ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen zakulo wadannan gurbatattun shugabanni tare da hukunta su daidai da abin da suka aikata.
Wadannan kalamai masu nauyi sun haifar da zazzafar muhawara tsakanin fadar mulkin Kenya da 'yan majalisar dokokin, inda suke ta jifan juna da miyagun kalmomi. Mambobin majalisar sun yi ta caccakar Shugaba Ruto da kakkausan harshe, kan wannan zargi. Wannan cece-kuce na kasar ta Kenya bai tsaya ga shugabanni kadai ba, domin har 'yan kasa ba a bar su a baya ba. Jeff Mwendwa ya nunar da cewa, kulba ce ke barna amma ake dorawa jaba laifi. Wani bincike da Hukumar Tabbatar da Da'a Tare da Yaki da Cin-hanci da Rashawa ta Kenya ta gudanar a bara, ya nuna yadda wannan matsala ta zama jiki a cikin dukkan al'amuran rayuwar yau da kullum a kasar.
Babban abin takaicin kuma shi ne, ba a samun masu shigar da korafi ga hukumomi domin tsawatar wa a kai. Wilson Sossion tsohon dan majalisar dokoki ne a Kenya, ya nuna rashin amincewarsa da yadda Shugaba Ruto ya yi wa 'yan majalisar kudin goro. Mafi-akasarin al'ummar Kenya na da yakinin cewa, akwai dokoki da suka yi tanadin tsauraran hukunce-hukunce ga masu aikata laifuka a kasar To sai dai babban tarnakin da ke zama dabaibayin aiwatar da hukuncin shi ne, rashin daukar matakan da suka dace daga bangaren masu rike da madafun iko.