1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIran

Iran: Ko Tehran na bunkasa nukiliyarta?

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 17, 2025

Iran ta bayyana cewa, a shirye take ta cimma matsaya mafi dacewa tsakaninta da kasashen Turai dangane da shirinta na nukiliya.

Iran | Abbas Araghchi | Nukiliya | Tattaunawa | EU
Ministan harkokin kasashen waje na Iran Abbas AraghchiHoto: Horacio Villalobos/Corbis/Getty Images

Ministan harkokin kasashen waje na Iran din Abbas Araghchi ne ya bayyana hakan, jim kadan bayan tattaunawar da suka yi da takwarorinsa na Birtaniya da Faransa da Jamus da ake wa lakabi da kasashen E3 da kuma jami'ar hulda da kasashen ketare ta kungiyar EU ta wayar tarho. Araghchi ya ce Tehran a shirye take ta cimma matsayar da za ta yi wa kowa dadi, sai dai ya ce kai wa ga hakan na bukatar taka-tsan-tsan wajen tunkarar lamarin daga kasashen Turan uku.