Burkina Faso: Sabon matakin kan batun tsaro?
April 30, 2026
Muhimmin aiki ne da gwamnatin mulkin sojan ta Burkina Faso ta sa a gaba, kafin karshen shekara tana da niyyar horar da dakarun ko ta-kwana guda 100,000. Majalisar ministoci ta wannan kasa da ke yankin Sahel ce ta amince da wannan daftarin doka, a wani mataki na karfafa tsarin tsaron kasar. A halin yanzu dai, rundunar sojojin Burkina Faso ta kunshi kusan jami'a 12,000. Wannan yana nufin cewar adadin sababbin dakarun ko ta-kwana zai ninka yawan sojojin kasar sau takwas. Bisa ga wannan tsarin za a fifita daukar ma'aikata da suke da kwarewa a fannin tsaro, yayin da za a bai wa sauran cikakken horo.
Mataki mai kyau, amma akwai sauran rina......
Léboure Crépin Zanzé kwararre kan tsaro a Dakar na Senegal ya ce, manufa ce mai kyau domin gwamnati na son aikawa da sako mai karfi. Amma ana bukatar jerin abubuwa, domin cimma nasarar samar da dakarun ko ta-kwana. Burkina Faso ta kasance karkashin jagorancin mulkin soja tun 2022, kuma gwamnatin da Kyaftain Ibrahim Traoré ke jagoranta ta yi alkawarin samar da tsaro sakamakon barazanar ta'addanci da take fuskanta. Sai dai har yanzu, ba a samu wani ci-gaban a zo a gani a wannan fannin ba. Masharhanta sun nunar da cewa, kusan kaso 60 cikin 100 na Burkina Faso ba ya karkashin ikon hukuma. Maimakon haka ma, kungiyoyin da ke da tsaurin kishin Islama kamar JNIM da sauran su na yawan kai hare-hare a kan sansanonin sojoji.
Hasali ma, duk kanwar ja ce a kasashen da ke cikin kawance AES kamar Mali da Nijar. Ko da a karshen makon da ya gabata, masu tsattsauran ra'ayi sun kai hare-hare a wurare dabam-dabam a fadin kasar Mali. Wannan dai ya raunana matsayi da kimar Rasha da ke kawance da kasashen Sahel, saboda an yi tsammanin za ta taimaka wajen tabbatar da tsaro a dukkan kasashen Sahel guda uku. Beverly Ochieng mai sharhi a Cibiyar Tuntuba ta Control Risks ta ce, Burkina Faso na son nuna za ta iya cimma nasara a fannin tsaro ba tare da taimakon tsofaffin abokan huldarta kamar Faransa ba.
Mataki cikin taka tsan-tsan
Amma ta ce sakamakon matsin lamba da take fuskanta a cikin da wajen kasar, ya zama wajibi ta yi sara tana mai duban bakin gatari. Sai dai diban dakarun ko ta-kwana na iya haddasa kalubalen tsarin bin umarni na soja, sakamakon rundunoni dabam-dabam da za a samu. Sannan za a iya samun rashin daidaito a tsakanin rundunoni lamarin da ka iya haifar da cin-zarafi, in ji kungiyoyin kare hakkin dan Adam na Burkina Faso.
Translated by Mouhamadou Awal Balarabe
Edited and Published by Lateefa Mustapha Ja'afar