1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIran

Ko Amurka ta cimma burinta a Iran?

Kersten Knipp SB
March 3, 2026

Bayan kisan jagoran addinin na Iran Ayatollah Ali Khamenei kasar ta shiga neman samun makoma. Shin za a samu sauyin shugabanci ko kuma madafun ikon kasar zai ci gaba da kasancewa a hannun dakarun kare juyin-juya hali?

Hoto: Atta Kenare/AFP/Getty Images

Mutuwar jagoran addinin na Iran Ayatollah Ali Khamenei ta zama mai tasiri ba kan kasra Iran kadai ba, har da sauran kasashen da ke yankin. Marigayin mai shekaru 86 da haihuwa ya rasa ransa sakamakon hare-haren dakarun Amurka da na Isra'ila. A cewar kundin tsarin mulkin kasar jiga-jigan malaman bangaren Shi'a 88 za su zabi mutumin da zai gaji marigayin.

Daga cikin 'yan   takara da ke kan gaba wajen neman maye gurbin Marigayi Ayatollah Ali Khamenei, akwai tsohon shugaban kasa Hassan Rouhani da dan-marigayin Mojtaba wanda yake makusancin rundunar kare juyin juya halin, kana akwai Hassan Khomeini jikan Marigayi Ayatollah Khomeini wanda ya kafa Jamhuriyar Musuluncin, kuma ya rasu a shekarar 1988. An kuma ambato sunan 'yan adawa mafi tasiri Reza Pahlavi dan Marigayi Shah da aka kifar a shekarar 1979. Ana daukan 'yan adawan Iran a matsayin masu rarrabuwan kai.

Iran Tehran 2026 | Majalisar Shugabancin wucin gadi ta gana da Shugaba PeseschkianHoto: Iranian Presidency Office/Apaim/APA Images/ZUMA/dpa/picture alliance

Kwamiti mai mutane uku  da shugaban kasar ya nada da ke karkashin jagorancin bangaren shari'a da wakilan majalisar shura. Amma tambayar zahiri ita ce, shin sauyin mutum za a yi ko kuma samun sauye-sauye na tsarin? Dakarun kare juyin-juya hali suna da tasiri wajen tafiyar da kasar duk da mutuwar kwamandansu Mohammed Papkur.

A cewar Bente Scheller ta Gidauniyar Heinrich Böllt a Jamus mutuwar Khamenei wata babbar alama ce, amma dai mutuwar dattijon mai shekarun 86 dawani abu ne da ba a yi tsammani ba. Yayin da Iran ke neman magajin shugabannin addinin, hanyar da ya mutu ke zama sabon lamari cikin batun.

Alireza Arafi, memba na majalisar tsaron IranHoto: irna.ir

Ita kuma Hanna Voß masaniya kan yankin Gabas ta Tsakiya a Gidauniyar Friedrich Ebert ta Jamus da ke da dangantaka da jam'iyyar SPD, tana ganin Shugaba Donald Trump na Amurka ya nuna rashin fahimtar kan abubuwa masu tasiri, saboda ya gaza fahimtar gwamnatin Iran da kuma madafun ikon kasar. Dakarun juyin juya-hali suna da bangaren leken asiri, gami da kungiyoyin masu dauke da makamai a ciki da wajen kasar.

A fili dai Shugaba Donald Trump na Amurka ya bukaci dakarun juyin-juya hali kan su ajiye makamai.

Donald TrumpHoto: Kevin Lamarque/REUTERS

Masanan suna ganin zai yi wuya a sauyin gwamnatin Iran. Amma akwai yuwuwar a samu sauye-sauye daga cikin tsarin. Duk yanayin da ake ciki Iran tana cikin mawuyacin hali tsakanin rushewar tsarin tafiyar da kasar da kuma ci gaba. Matakin gaba ya fi karfin kawai maye gurbin Marigayi Ayatollah Ali Khamenei, domin samun ci gaba da shugabanci a matakin kololuwa na kasar ta Iran.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani