Ina aka kwana a rikicin Isra'ila da Iran?
June 19, 2025
Yayin da ake ci gaba da gwabza fada da musayar hare-hare tsakanin Isra'ila da Iran, Tehran ta harba daruruwan makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuki zuwa wasu muhimman biranen Isra'ila. A wani harin da ya auka cikin asibiti a garin Be'er Sheva, fiye da mutane 40 sun jikkata ciki har da likitoci da marasa lafiya. An kuma samu raunuka a wasu sassa na Tel Aviv da Ramat Gan, sai dai duk da haka tsarin kariyar iska na Isra'ila wato Iron Dome ya dakile yawancin makaman da suka shigo sararin samaniyarta.
Karin Bayani: Iran-Isra'ila: Wace ce ke aikata fada ba bisa doka ba?
A matsayin martani, sojojin Isra'ila sun kai farmaki ta sama a cikin Iran, inda aka nufi wuraren da ake zargin ana ajiye makamai da kayan yaki musamman a garuruwan Isfahan da Arak da kuma Natanz. Rahotanni daga Iran sun tabbatar da hare-haren, amma sun ce ba a lalata cibiyoyin nukiliya ba. A halin yanzu, rahotanni daga Tehran na nuni da cewa fiye da mutane 600 sun halaka da yawa daga cikinsu fararen hula. Mutane da dama sun fara barin birane kamar Tehran na Iran da Haifa na Isra'ila domin tsira da rayuka.
A yayin da harin da Iran ta kai ya shafi asibitoci da dama a kudancin Isra'ila, daraktan asibitin Soroka da ke birnin Be'er Sheva Farfesa Shlomi Kodesh ya bayyana irin mummunan illar da makamin roka ya haddasa a ginin cibiyar lafiyarsu. A cewarsa wani makamin roka ya fada kai tsaye kan daya daga cikin gine-gine a cibiyar lafiya na bene shida, wanda yawanci ke dauke da daruruwan marasa lafiya. Harin ya rushe bene na biyar gaba daya, tare da yin illa ga gine-ginen da ke kasa da sama da shi.
Karin Bayani: Jamus: Ina makomar hulda ta Gabas ta Tsakiya?
Wuta mai tsanani ta tashi, wacce ta dauki sa'o'i da dama kafin a iya shawo kanta. Koda yake ya ce as lokacin harin babu kowa a cikin gine-ginen, saboda sun kwashe marasa lafiyar saboda dalilai na tsaro. Majalisar Dinkin Duniya da Kasashen Turai sun bukaci tsagaita wuta nan da nan, inda sakatare janar na majalisar ya bayyana damuwarsa game da rikicin da ke ci gaba da yin kamari. Shugaban Amurka, Donald Trump ya nuna goyon baya ga Isra'ila, inda rahotanni ke nuni da cewa yana duba yiwuwar kai mata agajin soja duk da yake har yanzu ba a yanke hukunci ba. A hannun guda kuma, tsoron yaduwar rikicin zuwa sauran kasashen Gabas ta Tsakiya na karuwa.