Kofofin Jamus a bude suke na cinikin makamai da Angola
August 23, 2018Gwamnatin Jamus a ta bakin shugabar gwamnati Angela Merkel, a shirye take ta sayarwa kasar Angola da makamai. Merkel ta bayyana hakan ne yayin ziyarar da shugaban Angola Joao Lourenco ya kawo birnin Berlin, tana mai cewa sayarwa Angola din makamai wani bangare ne na muradun Jamus na ganin Afirka ta kare kanta da kanta.
Da farko dai shugaba Joao Lourenco ya nuna cewa baya ga neman masu zuba jari na harkokin aikin gona da gina hanyoyi da fasaha kasarsa na neman tallafi a harkar sojoji.
"Muna gayyatar masu zuba jari daga Jamus ta yadda za mu yi aiki tare wajen ba da kariya ga gabar tekunmu, ko dai ta hanyar samar mana da jiragen yaki ko samun kayan lanturoni da za mu yi amfani da su wajen lura da iyakarmu ta ruwa inda 'yan fashin teku da 'yan ta'adda suke."
Angola ita ce kasa ta biyu mafi fitar da man fetir bayan Najeriya a Afirka, amma tana fama da matsalar faduwar farashin kayayyaki. Kasar na fadada hanyoyin da za ta rika samun kudin shiga da sauran huldodi da wasu kasashe ciki kuwa har da neman masu zuba jari daga Jamus.