Kogi: Muhawara kan zaben gwamna
November 23, 2015 Muhawara dai ta yi zafi tsakanin tsakanin 'yan siyasa da masana shari'a da kuma talakawa a Najeriya kan zaben Kogi wanda guda daga cikin masu zawarcin kujerar gwamnan jihar Prince Abubakar Audu ya rasu a Lahadin nan da ta gabata. Hukumar zaben kasar dai ta bayyana zabe a matsayin wanda bai kammala ba wanda hakan ke nufin cewar sai an sake zaben a wasu wurare.
Yanzu haka dai masana shari’a a duk fadin kasar na bayyana ra’ayoyin su mabanbanta kan wannan batu inda wasu ke neman a sake wannan zabe wasu kuma na cewa a nemi fassara daga kotu kan mafita a wannan yanayi. Barrister Muhammad Mai Lumo lauya kana masani kundin tsarin mulkin Najeriya na cewar ''kamata ya yi a ajiye wannan zabe a sake sabon lale.''
Shi kuma Barrister Abdullahi Muhammad Inuwa wanda shi ma masanin kundin tsarin mulkin kasar ne na ganin cewar mafita daya da ake da ita wadda kuma a ganinsa za ta kawo karshen wannan jayayya ita ce a dakatar da komai a nemi fassara daga babbar kotun tarayya Najeriya maimakon a yi ta fadin ra'ayoyi mabanbanta.
Su kuwa wasu ‘yan siyasa na da ra’ayin cewa tunda jam’iyyar APC na kan gaba, in har an kammala zaben kuma ta lashe sai a rantsar da mataikamkin Abubabakar Audu din a mastayin gwamna kana daga bisani shi kuma ya nemi wanda zai yi aiki da shi a matsayin mataimakinsa, sai dai wasu na cewar kyautuwa ya yi jam'iyyar APC ta sake zaben wani dan takarar gwamna sabo da zai maye gurbin marigayi Audu maimakon a ce za a ratsar da mataimakinsa.