Koizumi ya kai ziyara a Ethiopia
May 1, 2006Talla
Praministan ƙasar Japon, Yunichiro Koizumi, na ci gaba da ziyara aiki a ƙasar Ethiopia.
Bayan ganawar da yayi jiya,da Praminista Meles Zenawi , Koizumi ,ya bayyana wa manema labarai, mihimman batutuwan da su ka tantana.
Wannan batutuwa sun shafi, bukatar Japon, ta samun kujerar dindindin, a komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia.
Kazalika, ya bayyana goyan baya, ga ƙasashen Afrika, na samun wakilai a wanan komiti.
Nan gaba a yau, zai gana da magabatan ƙungiyar taraya Afrika, inda za su tantana wannan batu.