Kokarin Afirka na tura kwararru Burundi
September 28, 2017Talla
Wannan bukata ta kasashen ta biyo bayan fitar wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya wanda ya nuna irin yadda aka kashe mutane tare da azabtar da wasu wanda aka jingina yin hakan ga mahukuntan Bujumbura. Kasashen dai na son ganin kwararrun da za a tura su tantance zargin da ake yi wa gwamnati ta hanyar tattara bayanai kana su yi aiki da jami'an gwamnatin kasar da nufin rarrabe tsaki da tsaba. Kudurin ya samu amincewar kasashe 23 yayin da 14 suka nuna rashin amincewa sannan wasu kasashe 9 suka yi rowar kuri'unsu kuma an ajiye gobe Juma'a don yin muhawara da daukar matakin karshe kan batu.