Kaddamar da rundunar jami'an tsaro na jihar Kano
December 23, 2025
Babban taron aka yi a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar mata a tsakiyar birnin Kano, taro ne na kaddamar da matasa dubu biyu da aka bai wa horon tabbatar da tsaro domin cike gibin matsalar tsaro da ake fama da ita a jihar musamman ma farmakin 'yan bindiga da suka fara yi wa wasu kauyukan jihar dauki daidai.,
Da yake jawabi yayin kaddamar da matasan gwamnan Kano Engr Abba Kabir Yusuf ya hori jami;an da su zamo masu gaskiya da rikon amana, su kuma yi aiki tukuru domin dakile duk wata barazanar tsaro da ka ka iya tunkarar jihar,
Shi ma a nasa bangaren Dr Rabiu Musa Kwankwaso tsohon gwamnan Kano kuma tsohon kwamishinan tsaro na tarayyar Nigeria ya bukaci matasan da su dage wajen taimaka wa jami'an tsaro dan gudanar da ayyukan su.
Shi ma gwamna Dikko Rada na jihar Katsina, jihar da ke makotaka da Kano kuma ake ganin yawancin farmakin da ake kai wa kauyukan Kano daga Katsina ake shigowa ya bayyana cewra dole al'ummar arewa maso yamma su hade kai domin tunkarar matsalar rsaro a yankin.
Ana sa ran dai wadannan jami'ai za su yi amfani da makamai domin tunkarar masu kawo farmaki da makamai,sai dai masana shari'a irin su Barista Aminu Ibrahim ya ce dole batun bindiga sai an yi hattara kuma a yanzu baza'a kira wadannan jami'ai 'yan snadan jihohi ba
To shin ko kafa wannan runduna zai magance wannan matsalar tsaron da ake fama da ita, Dr yahuza Getso masanin tsaro ne da ke cewar gwamnan Kano ya yi kokari sai dai akwia sauran rina a kaba.
Duk da cewar tsanantar matsalolin tsaro ya sa jihohi na ta kirkirar rundunoninsamar da tsaro a yankunan su, amma masana na yin kira da a yi hattara kuma a kara samar da karin lura daga makotaka daga tushe domin magance matsalolin tsaron da ke girma su zama manya.