1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa za ta taimaka wajen yaki da Boko Haram

Lateefa Mustapha Ja'afarAugust 25, 2015

Shugaba Francois Hollande na Faransa ya ce zai shirya wani taro na kasa da kasa domin kawo karshen kungiyar Boko Haram da ta addabi Najeriya da makwabtanta.

Shugaban Faransa Francois Hollande da yaki da Boko Haram
Shugaban Faransa Francois Hollande da yaki da Boko HaramHoto: Reuters/P. Wojazer

Hollande ya bayyana hakan ne a wannan Talata yayin da yake ganawa da jakadun kasashen ketare a Faransan, inda ya ce nan ba da jimawa ba zai karbi bakuncin sabon shugaban Tarayyar Najeriyar Muhammadu Buhari, kana zai bashi tabbacin cewa Faranasa a shirye take ta hada karfi waje guda da dukkan bangarorin da ke yakar Boko Haram domin ganin an kawo karshen ayyukanta da ya hallaka mutane masu tarin yawa a Najeriya da sauran kasashen da ke makwabtaka da ita. Tuni dai kasashen Nijar da Kamaru da Chadi da kuma Najeriya suka kaddamar da wata rundunar hadin gwiwa da ake kira da "MNJTF" da za ta kunshi dakarun kasashen domin dakile ayyukan Boko Haram din. Kawo yanzu dai sama da mutane 15,000 ne kungiyar ta Boko Haram ta hallaka tun bayan da ta fara kai hare-hare a Najeriyar a shekara ta 2009.