Kokarin dakile matasa masu son zuwa Turai daga Najeriya
December 12, 2016Najeriya kasa ce da Allah ya yi wa baiwar albarkatu na kasa da na dan Adam, hatta da mutanen wasu kasashen na kusa da kuma na nesa suna kwararowa cikinta don su ci arziki su kuma bar arzikin a mazauninsa saboda yawa. Sai dai kwadayin kudancewa dare daya da rudin abokai ne ke sa matasan na Najeriya masu wannan burin na zuwa Turai ko ta wacce hanya, a kallon da suke yi wa Turan na tudun mun tsira, yin wannan warkajami fataucin tsumma da ba kasafai ake nasara kansa ba. Malam Aminu Hussaini wani matashi ne a nan Kano da ya taba gamuwa da rudin abokai duk da rufin asiri na sana'a da yake da shi. Haduwa da abokan tafiya a Nijar ne ya sa Aminu dogon buri na ketarawa zuwa Turai. Sai dai tun kafin isar su kasar Libya ya fara canza tunani ta la'akari da wadansu darussa daya karu dasu a hanya. Ya yi karin haske kamar haka:
"Ka ga wanda zai tafi nema ga wani ya dawo ko kuma wani yana waje ka je karuwa, amma ace shi a wajen ka yake nema, to tun lokacin na fara fahimtar cewa akwai matsala. To da haka dai har muka samu muka karasa, da muka karasa inda aka sauke mu ainihin masu saukar tamu sai na fahimci cewa so suke su sami kudin mota. Kokarinsu kawai ta kowane hali su dawo gida su dawo kasarsu."
Wadannan darussa da Aminu ya rika karuwa dasu ne ya sanya shi fasa tafiya inda ya lallashi wasu daga cikin abokan tafiyarsa suka dawo gida bayan kwanaki hudu a Libya. Matasa sun jima suna irin wannan kasada ta sayar da rai a Najeriya, amma ba tare da samo biyan bukata ba. Malam Ali Mashi shugaban wata kungiya ce ta rajin kare hakkin marasa karfi da taimaka musu wajen dogaro da kai a nan Kano. Ya ce wayar da kai da karfafa guiwar kama sana'o'in hannu a hukumar horar da sana'o'i ta kasa zai taimaka wajen hana irin wannan kasada da rai da matsan ke yi.