Shugabannin siyasa a Jamus sun amince da matakin karfafa dokokin haduwa da mutane, a kokarin dakile sabon nau'in cutar coronavirus da ake kira omicron.
Talla
Shugabannin siyasar na Jamus sun amince da wannan matakin ne, saboda kare tsarin lafiyar kasar daga shiga rudani ganin yadda sabon nau'in corona na omicron ke kara yaduwa. Ana dai sa ran za a yi aiki da matakan a yayin bukukuwan Kirsimeti da shiga sabuwar shekara, sai dai ba za a rufe daukacin harkokin rayuwa ba. Bayan wata ganawa tsakanin sabon shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da gwamnonin jihohi, sun amince cewa kar mutane su wuce 10 a yayin duk wata haduwa da za su yi.
An dai amince mutane 10 su hadu ne kawai, idan dukkansu sun yi riga-kafin cutar ta coronavirus ko kuma ba su dade da warkewa daga cutar ba. Ga wadanda ba su yi da riga-kafin corona ba kuwa, mutane biyu kacal aka amince su hadu. An dauki matakin sbaoda tsoron yaduwar cutar ta coronavirus lokacin bukukuwan da ke tafe, kuma sabon shugaban gwamnatin Jamus din Scholz ya yi karin haske ga al'umma: "Na fahimmci kowanne daga cikinku da ba ya kaunar jin kiran cutar corona da yadda take sauyawa zuwa wasu nau'o'i, amma ba za mu rufe ido kan yadda muka ga sabon nau'in cutar ya fara barkewa a tsakaninmu ba."
Hada-hadar Kirsmeti a lokacin corona
Bisa al'ada watannin Nuwamba da Disamba na zama mafi bunkasar ciniki ga kantuna da shaguna. Amma matakan kulle saboda corona sun janyo koma baya. Annobar ta shafi hada-hadar kasuwanci a Kirsmetin bana.
Hoto: Imago Images/Geisser
Koma baya a ciniki saboda corona?
Kirmetti na karatowa hakazalika lokacin hada-hadar kasuwanci, sai dai dokar kulle ta yi babban tasiri ga yadda Jamusawa ke gudanar da kasuwanci. Matakin rufe shaguna a Jamus a Kirsmetin bana ya shafi kasuwanci, wanda haka ya sa ciniki a lokacin bikin na bana ya yi rauni idan aka kwatanta da na bara. Tuni dai kantuna da shaguna suka tabka asara babba.
Hoto: Imago Images/Geisser
Ba a iya shiga gari don sayayya
Ba za a ga jama'a a cikin gari a lokacin shirye-shirye da hada-hadar Kirsmetti bana ba, saboda dokar kulle da mahukuntan Jamus suka kafa. Jama'a ba za su iya sayen kayan Kirsmeti a cikin gari ba. Sun koma ga yi ta yanar gizo. Ga masu kantuna da shaguna wannan yanayin ba mai dadi ba ne, domin hada-hadar kasuwanci a lokacin Kirsmetti ta fi sama musu kudin shiga.
Hoto: Rupert Oberhäuser/dpa/picture alliance
Ciniki ta intanet ya samu tagomashi
Sakamakon annobar corona, harkar kasuwanci ta intanet ta bunkasa sosai. A lokacin shirye-shiryen Kirsmeti ma harkar za ta ci gaba da bunkasa, za kuma ta zama abin farin ciki ga wannan bangare. Kungiyar 'yan kasuwa ta ce kasuwanci ta intanet zai karu da kashi 12 cikin 100 a wannan Kirsmeti, wanda ya yi daidai da Euro miliyan dubu 17 a hada-hadar cinikin ta Kirsmeti.
Hoto: picture-alliance/dpa/C. Schmidt
Boca ke kan gaba
Shin a bana me ake ajiyewa karkashin bishiyar Kirsmetti a Jamus? A nan ma kungiyar 'yan kasuwar Jamus ta yi hasashe. A sahun gaba: Boca ko Voucher. Yadda boca ke ba da damar zabi da yawa ya sa tana da farin jini ko a lokuta na rikici da rashin tabbas. An yi hasashe kashi 30 cikin 100 na Jamusawa za su samu bocarsu karkashin bishiyar Kirsmeti.
Hoto: picture-alliance/dpa
Sahu na biyu: Kayan wasan yara
Hada-hadar sayen kayan wasan yara ita ce a sahu na biyu a jerin kayayyakin da ke samun tagomashi suke kuma jan hankali na kyaututtuka. Yara dai na maraba da irin kyaututtukan kayan wasa da suke samu a lokacin bikin na Kirsmeti.
Hoto: picture-alliance/dpa/R. Weihrauch
Litattafai da kayan rubutu
Sahu na uku shi ne litattafai da kayan rubutu, da ke zama abin jan hankali na kyaututtuka. A cikin wannan rukuni ma kusan kowa zai samu rabonsa. Bisa hasashen kungiyar ciniki ta Jamus kashi 26 cikin 100 na Jamusawa za su samu kyautar littafi ko abin rubutu ko sauran kayan rubutu karkashin bishiyar Kirsmeti.
Hoto: picture-alliance/dpa/U. Anspach
Kayan kwalliya da kayan gyaran jiki a sahu na hudu
Daga ruwan sabulun wanka zuwa man shafawa har su jan baki da kyallen rufe fuska: Kashi 20 cikin 100 na Jamusawa za su yi murna da kayan kwalliya da na gyaran jiki a lokacin bikin. Za su iya yin tsada, a takaice a bana masu amfani da kaya za su kashe Euro 330 wajen sayen kayan kyauta a cewar masu nazarin harkokin kasuwanci na GfK.
Hoto: Jens Kalaene/dpa/picture alliance
Tsabar kudi karkashin bishiya
Za a ajiye tsabar kudi karkashin bishiyar Kirsmeti. Kimanin kashi 19 cikin 100 na Jamusawa za su yi farin ciki da wannan. Saboda yana a sahu na biyar a cikin kyaututtuka da aka fi so. A binciken jin ra'ayin jama'a da kungiyar ciniki ta yi a dukkan bangarorin ta gano irin kayayyakin kyauta da al'umma ke so. Daga cikin 10 da aka fi so har da tufafi da kayan abinci da kayan ado.
Hoto: picture-alliance/dpa
Hattara wajen sayen kaya ta intanet!
Musamman ya kamata a yi hattara da sayen kayan lanturoni ta intanet. Hukumar kula da wayoyi ta tarayyar ta yi gargadi game da kaya masu hadari musamman daga kasashen Asiya, da sau da yawa ba sa cika ka'idojin ingancin kaya kamar yadda doka ta tanada. A wasu lokutan ana samu hadura masu barazana ga lafiya. Za a iya kare kai idan aka saye daga amintattun kamfanoni masu kuma gaskiya.
Hoto: Picture-Alliance/Shawn L. Minter via AP
Hotuna 91 | 9
Rige-rigen sayen kayayyakin kyaututtuka da ake bayarwa lokacin bukukuwan na Kirsimeti da sabuwar shekara domin mikawa ga 'yan uwa da abokan arziki, za su ci gaba da kasancewa kamar yadda aka saba kasancewar sabon matakin mahukuntan Jamus zai fara aiki ne a ranar 28 ga wannan wata na Disamba. za a gudanar da bikin sabuwar shekarar shiru, ba kamar yadda aka saba ba ta hanyar yin wasanni a wuraren da babu 'yan kallo da kuma rufe gidajen rawa.
Gwamnati tana fatan ganin samun ci gaba ta fuskacin yin riga-kafi zuwa lokacin bikin Kirsimeti. Ana fatan yin milyoyin riga-kafin zuwa watan Janairu mai zuwa. Sabon shugaban gwamnatin Jamus din ya ce ana samun raguwar masu kamuwa da cutar ta coronavirus,gabanin bullar sabon nau'in na Omicron. Cutar dai ta kassara armashin bikin Kirsimetin, kuma ga 'yan siyasa akwai sauran aiki kan irin yadda za su tunkari al'umma.