1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

OPEC ta cimma matsaya kan daga farashin man fetur

Ramatu Garba Baba
June 4, 2023

Kasashen Rasha da Saudiyya sun amince su rage yawan man da suke fitarwa zuwa kasuwannin duniya a kokarin da suke na farfado da farashin mai.

Tutar Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur (OPEC)
Tutar Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur (OPEC) Hoto: ALEXANDER KLEIN/AFP/Getty Images

Kasashen Rasha da Saudiyya sun amince da sabuwar dokar rage yawan man da suke fitarwa zuwa kasuwannin duniya, sun dai yi hakan ne don amsa kiran Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC da ta shawarci a yi hakan saboda faduwar da farashin na man fetur yi a taron da ta kira a wannan Lahadin a birnin Vienna na kasar Austria.

Mambobin kungiyar 13 da wakilan Rasha da ke kawance da kungiyar ne suka gana a kokarin shawo kan matsalar, al'amarin da ya janyo karancin bukatar man a kasashe da dama saboda tabarbarewar tattalin arzikinsu.