Yunkurin hana yaki a nahiyar Turai
February 9, 2022Talla
Shugabannin kasashen guda uku wadanda suka gana da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Cholz a birnin Berlin sun ce ba za su bari ba a shiga yin yaki da Rasha. A lokacin da yake magana da manema labarai bayan tattaunawarsu da shugabanin Faransa da kuma Poland shugaban gwamnatin Jamus Olaf Cholz ya ce za su yi ruwa su yi tsaki a kan wannan batu har sai sun tabbatar da zaman lafiya a tsakanin Ukraine da Rasha.