Turai da Indiya za su inganta kasuwanci da tsaron yankunansu
April 24, 2022Talla
Ursula von der Leyen ta soma rangadin da yada zango a wata cibiyar samar da makamashi da ke Delhi inda ta gana da wasu matasa 'yan fafutuka kan sauyin yanayi, daya daga cikin ilollin da duniya ke fuskanta a yanzu.
A ranar Litinin mai zuwa, za ta gana da Firaiminista Narendra Modi inda za su tattauna batutuwa da suka shafi bunkasa kasuwanci da tsaro da kokarin ceto duniya daga matsalolin gurbatar yanayi, wanda Turan ta sha fadi sai an hada karfi kafin a iya cimma nasara.
Wannan dai na zuwa ne, a daidai lokacin da Indiya da Chaina ke ci gaba da shan suka daga manyan kasashen duniya saboda yadda suka yi gum kan mamayar Ukraine da Rasha ke yi.