1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin inganta ilimin makiyaya a Najeriya

March 16, 2017

A jihar Katsina wani Bafulatani wanda ya yi karatun boko mai zurfi ya dukufa wajen fadakar da 'yan uwasan Fulani makiyaya kan su rika sa yayansu makarantun boko inda rashin ilimin ya kawo cikas a sanin al'amuran duniya

SOS Kinderdorf in Gambia
Hoto: dpa

Shi dai wannan Bafulatani Mannir Atiku Lamido, yana hubbasan ganin 'ya'yan Fulani sun samu ilimin boko dan a dama da su a harkar rayuwa gami da fadakar da yan uwasan Fulani illar tallar nono da matansu ke yi a kasuwannin.

"Babu cigaba babu rayuwa ingantatta ga duk al'ummar da bata da ilimi, wannan ilimi an yadda duk duniya bata ci gaba idan babu shi. Amma har yanzu wasu fulani makiyayan basu saki jiki ba"

Matsayinka na Bafulatani, ta yaya ka ke ganin ilimin boko zai amfani Bafulatani wanda ko da yaushe rayuwarsa a daji ta ke?

"Ilmin nan zai yi fa'ida musamman ga diyan Fulani wadanda a zamanin yanzu matsaloli suka da bai baye, ta hanyar lalacewar dabi'um yayansu matasa da kuma munanan abubuwa da ke faruwa da diyansu"

A fafutukar da Lamido ke yi na ganin fulanin sunsa yayansu makarantun boko, yana kuma fadakawar ganin fulani sun dakile matansu daga zuwa tallace-tallacen nono cikin kasuwannin birane, wanda a cewarsa rashin wannan ilimin shi ke kawo haka

"Wannan talla da yayan Fulani ke yi da aurensu wallahi yana cikin abunda ke ci mana tuwo a kwarya. Saboda mun yi imani yana daga cikin abunda ya jawo gurbacewar dabi'u yan uwanmu, bayan wannan matsalar ta rashin ilimi wadda rashin ilmin shi ke sawa mutum ya saki matarsa bakatatan ba tare da yin la'akari da cewa me ka iya faruwa da ita"


Shin ko yaya fulanin ke kallan wannan fadakarwa wadannan wasu fulani da suka bayyanawa DW ra'ayoyinsu
"Sunana Aliyu Muhammad Fitoji kiran da nake yi kan yan uwa Fulani su sa yayansu makarantu musamman na zamani dama na addinin, kada a barsu a baya saboda duka rayuwa gaba daya bata cigaba sai da ilimi"

Shi ma dai wannan magidanci cewa ya yi: "Sunana Alhaji Abdul-Kareem mai Shoda shi ilimi da ka ke gani duk wani Bafullacen kasar nan idan yana da ilimi babu abun da zai gagare shi. Abun da ya sa muka koma koma baya ke nan, saboda rashin ilimin nan. babu wata kabila da za ta samu rayuwar duniyar nan in ba tare da ilimi ba"