1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin karfafa danganta tsakanin Jamus da Afirka

Dagmar Engel/UANovember 23, 2015

Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya kai ziyararsa ta biyar cikin shekaru biyu nahiyar Afirka da nufin karfafa dangantaka ta kasuwanci tsakanin bangarorin biyu.

Frank-Walter Steinmeier Besuch Mosambik Afrika Maputo Ernesto Max Tonela
Hoto: picture-alliance/dpa/B.von Jutrczenka

Yayin ziyarar ta Steinmeier, babban sakataren kungiyar hadin kan tattalin arziki ta kasashen Afika ta gabas Richard Sezibera ya ce burin hadin kai tsakanin Jamus da kasashen dai shi ne cin ribar juna inda ya ce kasashen Afrika suna bukatar shigar da kayayyakinsu zuwa kasuwannin Jamus. Bugu da kari kuma ya ce nahiyar ta na sha'awar musayar fasaha tsakanin bangarorin biyu. A karon farko an ga alamu na samun hadin kai daidai wa daida tsakanin kasar ta Jamus da kasashen na nahiyar Afrika, kamar yadda shi kansa Steinmeier ya sha nunarwa.

Ministan harkokin wajen na Jamus dai ya sami rakiya a lokacin ziyarar a wannan karo daga wata tawaga mai karfi mafi yawansu kanana da matsakaitan yan kasuwa da masu masana'antu wadanda suke da sha'awar shiga kasuwannin nahiyar Afika. Shugabar kamfanin Siemens a Afirka ta Kudu Sabine Dall'Omo ta ce burinta shi ne t samu gagarumin filin da za ta kafa reshen kamfanin na ta a Mozambique yadda za ta shiga al'amuran ciniki da kasuwancin dimbin arzikin gas da Mozambique din ta ke da shi.

Batun sufuri da makamashin na daga cikin abubuwan da aka fi maida hankali a kai lokacin ziyarar ta SteinmeierHoto: picture-alliance/dpa/B.von Jutrczenka

A Kampala babban birnin kasar Yuganda, akwai wani shiri na gina sabuwar tashar jiragen ruwa a Bukasa, shirin da kamfanin nan mai suna Gauff ya yi shekaru bakwai ya na tattaunawa kansa da gwamnatin kasar ta Yuganda. Idan har aka gina tashar, za ta hade Kampala da tashar jiragen ruwan Tanga da Daresalam, maimakon a yanzu duk kayayyakin da ke shiga yankin sai sun bi ta tashar jiragen ruwan Mombasa a kasar Kenya.

Batun bada toshiyar baki kafin a sanya hannu kan kwantaragin gina tashar jiragen ruwan a Bukasa bai ma taso ba, inji shugaban kamfanin na Gauff. To amma duk da haka batun cin rashawa na daga cikin manyan al'amuran da aka maida hankali kansu a lokacin wannan ziyara ta Steinmeier a nahiyar Afika har ma ya ke cewar "yaki da cin rashawa a mafi yawan kasashen na daga cikin al'amuran da muka duba, inda kuma muke sa ran za a kara maida hankali kan wannan matsala.''

Bayan da ya yada zango a Tanzania, minista Steinmeier ya koma Berlin. A nan Jamus dai babu wata sha'awa da aka nuna sosai tattare da ziyarar ta ministan a Afrika. Hakan kuwa watakila na tattare ne da hare-haren da 'yan tarzoma suka kai a birnin Paris. Ziyarar ta dauki hankali ne kawai bayan da 'yan ta'ada suka kai tare da garkuwa da mutane a Bamako na kasar Mali.

Cin hanci da rashawa da aiyyukan ta'addanci na kan gaba wajen dakile irin cigaban a Afirka.Hoto: picture-alliance/dpa/B.von Jutrczenka

A karshen ziyarar ta sa dai Steinmeier ya nunar da abin da ake nufi da dangantaka ta kafada da kafada tsakanin Jamus da Afirka inda ya ke cewar "fatan da kasashe da kungiyoyin duniya su ke yi shi ne na ganin kokarin sulhu da kasashen Afrika''.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani