Yayin da farashin man fetir ke ci gaba da zama a yanayi na rashin tabbas gwamnatoci a Najeriya musamman a matakin jihohi na duba wasu hanyoyi da za su dogara a kansu dan samun kudade.
Talla
Tuni dai wasu jihohi na Najeriya irinsu Katsina da Jigawa ke duba sabbin dabaru dan inganta tattalin arzikinsu ta hanyar neman masu zuba jari a fannin noma da wasu albarkatun kasa.