1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Senegal: Yakar ayyukan tarzoma

Umaru AliyuFebruary 3, 2016

'Yan sanda a Senegal sun binciki mutane akalla 900, sakamakon hare-haren da 'yan tarzoma suka kai aOuagadougou na kasar Burkina Faso a tsakiyar watan Janairu

Symbolbild Mädchen Frauen Salafismus
Hoto: picture-alliance/dpa/B. Roessler

A kasar ta Senegal yanzu haka dai jami'an tsaro suna horad da karin yan sanda kimanin 1000, wasu daga cikinsu a fannin yaki da aiyukan tarzoma. Hakan yana gudana n duk da ganin cewar Senegal tana daya daga cikin kasashe dake da kwanciyar hankali, inda addinin musulunci da mafi yawan yan kasar suke bi, ba ya fama da atsalar aiyukan tarzoma. Boukary Sambe na jami'ar Gaston Berger a St. Louis na Sebnegal, ya kwatanta kasrsa a matsayin wadda ta zama dabam da sauran kasashe na musulmi.

Yace a yan shekarun baya-bayan nan, Senegal ta zama wani tsibiri na zaman lafiya da kwanciyar hankali, a tsakiyar wani teku inda rashin tsaro da rashin kwanciyar hankali suka yi kakagida a Afirka ta yamma. Wannan kuwa yanayi ne da ya samu, godiya ta tabbata ga tafarkin darikar Sufi da kasar take bi. To amma ina da ra'ayin cewar hare-haren da aka kai a Ouagadougou sun zama alamar kawo karshen wannan kwanciyar hakali.

Masana sun yi kiyasin cewar tun a shekaru na 50 ake da kungiyoyi masu tsanancin ra'ayi a kasar ta Senegal. An sami bullar sabbin kungiyoyi da akidoji a kasar, sakamakon angizon Saudi Arabia a can. Yayin da mabiya akidar Wahabiya da Salafiya suka dade suna zauna lafiya da takwarorinsu masu bin akidar Sufi, amma a yanzu ana tsoron yiwuwar samun karuwar manufofi na matsanancin ra'ayi. Ute Gierczynski Bocande ta cibiyar Konrad Adenauer a Dakar, tace ta lura da karuwar gibi tsakanin masu arziki da matalauta a kasar ta Senegal, yayin da a lokaci guda, fannin bayar da ilimi yake kara samun rauni, abin da ya sanya ake kara samun matasa dake janyewa zuwa makarantun Islamiyya ko jami'oin kasashen Larabawa. Abin da ya zama sakamakon haka kuwa shine matasan basu da wata dama ta samun wuraren aikin yi a kasar, inda harshen Faransanci ya zama wajibi.

Hoto: picture-alliance/dpa/B. Roessler

"Tace wannan ba ma yana kawo rashin gamsuwa ne tsakanin masu fama da talauci a kasar ba, amma har a tsakanin masu hannu da shuni da masu ilimi, wanda abu ne mai matukar hadari. A baya-bayan nan ana kara ganin yada matasa suke kara shiga kungiyoyi da darikoki masu matsananin ra'ayi, wadanda kuma suke tsananta bin dokoki da shari'ar Islama tsakanin jama'a. Irin wadannan matasa cikin ruwan sanyi ana iya daukar su zuwa ga kungiyoyi na yan ta'adda.

Shi kuwa Daouda Gueye ya baiyana halin da ake ciki ne a wani yanki mai suna Pikine, da ke da matsalar rashin iya karatu da rubutu daambaliyar ruwa, yayin da garin yake da jama'ar da suka fi karfin da zai iya dauka a cikinsa. Gueye yana tafiyar da wani gidan rediyo ne mai suna Radio Oxyjeunes, dake maida hankalinsa ga matasa na wannan yanki. yace ya lura da samun canji tsakanin matasa ya zuwa ga bin tafarkin addini tsantsa. Yace mun lura a nan yankin Pikine cewar matasa suna kara nuna sha'awarsu ga tafarkin Salafiya, inda ya kara da cear a ra'ayinsa, ilmantarwa zai taimaka ga rage wannan tafarki na matsanancin ra'ayi.