1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin kawo karshen juyin mulki a Afirka ta Yamma

Salissou Boukari M. Ahiwa
December 5, 2022

Batun samar da rundunar tsaro da ECOWAS ke yi, na ci janyo martani daga 'yan siyasa da kungiyoyi masu zaman kansu a Nijar ganin yadda ake cece-kuce kan rashin mulki na gari.

Taron shugabannin kasashen ECOWAS
Taron shugabannin kasashen ECOWASHoto: FRANCIS KOKOROKO/REUTERS

Za a iya cewa tuni dai ra’ayoyi suka bambamta dangane da wannan mataki na kungiyar ECOWAS game da samar da rundunar tsaro da aka jima ana cece-kuce a kanta. Bisa tsarin kungiyar, rundunar za ta samu hurumin martani ga duk wani juyin mulki da za a yi a daya daga cikin kasashe mambobinta.

Tuni dai a fuskar ‘yan siyasa ra’ayoyi suka sha bambam inda, Sahnine Mahamdou, wani jigo a jam’iyyar da ke mulki a Nijar, ya ce ECOWAS ta makaro wajen samar da wannan runduna. Amma fa Kane Habibou Kadaure shugaban jam’iyyar SDR Sabuwa da ke bangaran adawa, cewa ya yi gudanar da kyakkyawan mulki ne kawai zai hana juyin mulki.

Hoto: Iancuba Dansó/DW

Wannan tunani na gudanar da mulki na gari, shi ma Nayoussa Djimraou na kungiyar farar hula ta MPCR na da wannan ra’ayi.

Sai dai da yake tsokaci kan wannan batu, Malam Nassirou Seidou na kungiyar muryar talaka, cewa ya yi dole ne a dauki wannan mataki domin kare mutucin Afirka.

Abin jira a gani dai shi ne tasirin da wannan runduna ta ECOWAS za ta yi idan aka yi la’akari da rundunoni irin su G5 Sahel da suka kasa kai labari ta dalilin samun kudaden aiki duk kuwa da matsalolin tsaron da ake fuskanta a yankin Sahel.