1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar almajirai na kara yawa a Najeriya

October 14, 2019

Wani taron masana a Kaduna da ke arewacin Najeriya ya duba hanyoyin magance matsalar bara tsakanin yara almajirai a yankin arewacin kasar.

Nigeria Koranschule Schüler
Hoto: DW

Zauran  taron dai ya cika da masana da manazarta daga jami'o'i dabam-dabam da hukumomi da Sarakunan Arewa tare da malaman makarantun allo da na Islamiyya daga yankin, inda aka tattauna kan irin matakan da suka kamata a dauka don shawo kan wannan matsalar.


Taron shi ne irinsa na farko da aka gudanar na tsawon kwanaki biyu kan matsalolin almajiranci da kalubalen da ke addabar ilimin kananan yara almajirai a daukacin arewacin kasar, inda aka yi waiwaye gami da yadda al'amarin yake a jiya da yau da nufin inganta daukacin makarantu allo.


Dr Sani Ibrahim wani malami ne da ke karantar da harshen Labarabci a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, wanda kuma ya kasance daya daga cikin wadanda suka gabatar da kasida wajen taron. Ya nunar da cewa ya zamo mana wajibi a fito da sabbin dabarun hanyoyin magance wannan lamari da ke shafar ilimin yara almajirai. A ganinsa lokaci ya yi da dukkanin masu kishin Arewa da masu ruwa da tsaki daga wannan yankin za su  tashi tsaye domin taimaka wa bangaren ilimin wadannan kananan yara da ke gararamba da kokon bara wajan neman abinci yayin da suka shigo biranen kasar don neman ilmin Arabiyya.


Masanin ya ce akwai bukatar bambamta tsakanin bara da karantun almajiranci, domin ba haka yake ba a shekarun baya. 
Daga cikin batutuwan da aka tattauna sun hada da daukar yara zuwa ci-rani inda da suke fadawa cikin wani yanayi maras kyau. Akwai bukatar samar da makarantun Islamiyya a yankunan da aka fi samun yawan almajirai domin dakile kwararowarsu zuwa birane.

Da yawa daga cikin yaran makarantun allo kan yi bara don samun na sakawa bakin salatiHoto: DW


Alhaji Saidu Mohammed Balarabe shi ne kwamishinan kudi da ya wakilci gwamnatin jahar Kaduna, ya ce kashi 98 cikin 100 na almajiran da ke Kaduna, daga jihohi makwabta suka fito, lamarin da ya sanya gwamnatin daukar matakai ciki har da ganin cewa an fara maida wadannan yara jihohinsu na asali.

Mallam Rabiu Abdullahi daya ne daga cikin shugabannin makarantun allo da ya ba da ya yi kira ga gwammanti da ta tallafa wa ilimin yara almajirai ta hanyar ba su wani filin noma domin ciyar da kansu da kuma ba su kulawar da ta kamata.