1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin neman mafita a Najeriya

September 28, 2017

A Najeriyar sassa daban-daban na masu ruwa da tsaki sun kaddamar da tattaunawa a tsakanin manya da kabilu na kasar da nufin  neman mafita ga makomar kasar.

Mataimakin shugaban Najeriya da wakilan majalisar ministoci na kasa
Mataimakin shugaban Najeriya da wakilan majalisar ministoci na kasaHoto: Novo Isioro

Har ya zuwa yanzun dai babbar matsala a tsakanin 'yan mulki dama talakawa a Najeriyar dai na zaman amsa tambaya muhuimmiya guda game da gamsuwa da yadda tsarin kasar ke tafiya a lokaci mai nisa. Duk da cewar dai an doshi shekaru har 60 ana faduwa ana sake tashi, hankoro na kuma kara karuwa tsakanin masu neman da a ware da masu tunanin sake tsarin da muryarsu ke kara karfi cikin kasar a halin yanzu.

Manyan 'yan boko da 'yan siyasar na Najeriya sun hadu suka yi tunanin cewar akwai bukatar a samu mafita ga halin da kasar take cki a karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Najeriya General Yakubu Gowon. Farfesa Jerry Gana dai na zaman daya a cikin wakilai daga yankin arewa ta tsakiya a cikin  wata tattaunawa da kungiyar tattaunawa da ci gaba mai zaman kan ta da ke a Abuja ta kai ga shiryawa da nufin nazarin bukatu na 'yan kasar sannan kuma da neman hanyar dorawa cikin kokarin ginin kasar da ke neman rushewa.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW