Kokarin neman sulhu a rikicin Siriya
January 25, 2018![Astana Neue Friedensgespräche zu Syrien-Konflikt](https://static.dw.com/image/41907871_800.webp)
Talla
Wannan tattaunawa dai na zuwa a daidai lokacin da fada ke kara yin muni tsakanin dakarun gwamnatin da na 'yan tawayen a fagen dagga abin da ake gani zai iya yin kafar ungulu ga shawarwarin. Daman dai wata guda da ya wuce an gudanar da irin wannan taro a Geneve ba tare da samun daidaito ba tsakanin bangarorin biyu sakamakon yadda aka gaza yin tattaunwa ta gaba da gaba.