Kokarin sake daukar fasali a cikin jam'iyyar PDP
October 29, 2013A wani abun dake zaman alamu na tabbatar rudani a tsakanin 'yan bakwai na sabuwar PDP, a kalla daya a cikin gwamnonin bangaren ya kama hanyar komawa gidan wadata domin aiyyana biyayya da da'ar sa ga shugaban PDP Bamanga Tukur da a baya bangaren ya ce barinsa na zaman wajibin kawo karshen rikicin.
Sannu a hankali dai ruwan yana kara tsami sannu a hankali kuma su kyalla sun fara gane dawan garin su a sabuwar PDP da a baya ta hade wajen adawa da manufofin jamiyyar PDP amma kuma kanta ya kai ga rabewa tsakanin masu shirin barin jamiyyar da kuma masu shirin komawa don tuba ga masu gidan na wadata.
Duk da cewar kwai da kwarkwatar mabiyan na sabuwar PDP dai sun yi garin Sokoto a kokari na tabo alli dama kila tunanin hanya ta gaba, ana saran can a garin Mina gwamnan jihar Dr Muazu Babangida Aliyu na shirin tuba a cikin laifukan da ya ce ya yi wa PDP tare da mai da kansa cikin 'ya'yan da ke biyayya ga Bamanga Tukur.
Babban dalilin komawar sa tsohuwar shekar da ya ke shirin fadawa talakawan jihar ta Nijer dai na zaman tsoron rashin magaji a shekara ta 2015, dama kwace masa jama'a a nan gaba.
Dalilan kuma da suka haifar da Owambe cikin gidan na wadata da ya dauki lokaci yana fuskantar tashin hankali, amma kuma ya kama hanyar komawa dai dai a fadar Barrister Abdullahi jalo da ke zaman mataimakin kakakin Jamiyyar na Kasa.
Tsalle -tsalle ga siyasa ko kuma kokari na sake daukar fasali a cikin PDP, in har a tunanin Gwamnan Aliyu sulhu da 'ya'yan na wadata na zaman mafita ga makoma ta siyasar sa, ga dan uwansa Murtala Nyako da ke zaman gwamnan Adamawa, babban kuskure ne ga tunanin PDP za ta bada mama ranar da su Aliyun ke matukar jin yunwa da kishirwar mulki a zabukan na shekara ta 2015.
Ana dai kallon raba garin a matsayin gagarumin koma baya ga 'yan bakwan da a cikin kasa da tsawon shekara guda suka yi nasara tada hankulan da babu irinsu cikin tarihin PDP na shekaru kusan 15.
To sai dai kuma a fadar Garba Umar kari dake zaman masani na siyasar kasar ta Najeriya, raba garin ba yana nufin karshen tawayen da ke zaman irin sa mafi tasiri ga kokarin sauya salon siyasar kasar ta Najeriya.
Har ya zuwa ranar yau dai babu bukata koda kwaya daya cikin takwas da 'yan tawayen suka yi nasarar mika wa shugaban kasar da ta samu shiga balle amfana da nufin dorin PDP a matakin gyara da cigaba.
Mawallafi: Ubale Musa
Edita : Zainab Mohammed Abubakar