Kokarin samar da sabuwar gwamnati a Maroko
March 26, 2017Talla
Firaminista Saad-Eddine El-Othmani ya ce ba da dadewa ba za a fitar da jerin sunayen sabbin membobin gwamnatin da za ta kunshi mutane daga jam'iyyu shida na hadaka. Sabuwar gwamnatin ta Maroko za ta kunshi 'yan jam'iyyar PJD (Parti justice et Developpement), da abokiyar kawancenta jam'iyyar PPS ta masu ra'ayin kwaminisanci, da jam'iyyar RNI ta masu sassaucin ra'ayi, da jam'iyyar "Mouvement Populaire" MP, da "Union Constitutionnelle" ta UC da kuma jam'iyyar USFP ta 'yan Socialiste, a cewar Firaminista El-Othmani yayin wani taron manema labarai a birnin Rabat. Firaministan ya kara da cewa a wannan Lahadin ne za a kafa kwamitin da zai dukufa wajen zaben sabbin ministocin da kuma rubuta tsarin tafiyar da harkokin gwamnatin.