Fafutukar cimma daidaito a Libiya
January 22, 2021Talla
Taron wanda ake yi Bouznika a kudancin Maroko ya hada 'yan majalisun dokokin na Tabruk wanda ke a karkashin ikon janar Haftar da kuma wandanda ke yin biyaya ga gwamnatin wucin gadi da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya. Kasar Libiya ta fada cikin wani hali na rishin tsayayyar gwamnati tun bayan faduwar gwamnatin Muammar Kadhafi a shekara ta 2011.