1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa: Sasanta Azerbaijan da Armeniya

Lateefa Mustapha Ja'afar
April 28, 2023

Faransa ta bukaci mahukuntan Azerbaijan da su cire shingen binciken da suka sanya a mashigar Lachin, hanya daya tilo ta kasa da ta hada Armeniya da yankin Nagorno-Karabakh da kasashen biyu ke rikici a kai.

Armeniya | Lachin | Nagorno-Karabakh | Azerbaijan | Rikici
Hanyar kasa tilo ta Lachin, wadda ke hada Armeniya da yankin Nagorno-KarabakhHoto: Tofik Babayev/AFP/Getty Images

Ministar harkokin wajen Faransan Catherine Colonna ce ta yi wannan kira, yayin wani taron manema labarai a Yerevan babban birnin kasar Armeniya. Ziyarar tata a Armeniya na zuwa ne jim kadan bayan tattaunawarta da shugaban kasar Azerbaijan Ilham Aliyev a fadarsa da ke birnin Baku, inda ta ce ya kamata a girmama martabar yankunan Armeniyan. A nasa bangaren takwaranta ministan harkokin waje na Armeniyan Ararat Mirzoyan ya bayana cewa, tilas a dawo da 'yancin zirga-zirga a yankin. Azerbaijan dai ta sanya shingen ne a Lahadin karshen mako, matakin kuma da makwabciyar kasa Armeniya da ke zaman abokiyar hamayyarta ta tir da shi. Kassashen biyu da ke makwabtaka da juna, sun kwashe tsawon lokacin suna rikici a kan yankin nan na Nagorno-Karabakh da ke kan iyakokinsu.