Kokarin sasanta Iraqi da Turkiyya ya dau hanya
November 2, 2007Talla
Sakatariyar harkokin wajen Amurka CR ta gana da Faraministan Turkiyya Recep Tayyip Erdogan. A lokacin tattaunawar, CR tayi kokarin janyo hankalin mahukuntan na Ankara ne, wajen ajiye matakin yin kutse ne a Iraqi.Mahukuntan na Washinton na tunanin cewa aiwatar da wannan kutse, ka iya kara rura wutar rikice rikice, a kasar ta Iraqi. A yanzu haka dai Turkiyya na da dakarun soji zambar dubu dari, a iyakar kasar ta ta da Iraqi. Sojojin a cewar rahotanni na jibge a matsayin shirin kota kwana na afkawa yan tawayen kurdawan dake boye ne a arewacin kasar ta Iraqi. Tuni dai CR ta isa birnin Istanbul don halartar taron koli kann kasar Iraqi.