1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-hare a yankin sinai na Masar

Lateefa Mustapha Ja'afarJuly 2, 2015

Gwamnatin kasar Masar ta kaddamar da kai hare-hare ta sama da jiragen yaki a yankin Sinai domin fatattakar 'yan kungiyar IS.

Ruwan makamai a birnin Sinai na Masar
Ruwan makamai a birnin Sinai na MasarHoto: picture-alliance/AP Photo/A. A. Schalit

Rahotanni daga majiyoyin tsaron kasar sun tabbatar da cewa akallah mayakan na IS 23 ne suka sheka barzahu a hare-haren, bayan kwashe tsahon yini guda suna gwabza kazamin fadan da aka bayyana da mafi muni a yankin cikin wannan shekara. Majiyar ta ce wadanda aka kashe din na daga cikin 'yan ta'addan da suka fafafata da dakarun gwamnati a jiya Laraba a gumurzun da ya hallaka mayakan masu tarin yawa da kuma sojojin kasar. Tsagerun yankin na Sinai da ke da alaka da kungiyar 'yan ta'addan IS sun zafafa kai hare-hare a kan sojoji da 'yan sandan Masar din tun bayan da shugaban kasar mai ci yanzu Abdel Fattah al-Sisi ya jagoranci kifar da gwamnatin tsohon hambararren shugaban Masar din Mohamed Mursi a shekara ta 2013.