Kokarin tsige shugaban kasar Somaliya
August 20, 2015Talla
A cewar wani dan majalisa Abdi Barre Yusuf, daya daga cikin masu goyan bayan a tsige shugaban kasar, wannan mataki na gyara ne suke kokarin dauka, ba wai na batawa ba. 'Yan majalisun dokokin na Somaliya dai na zargin shugaban kasar da hannu cikin harkokin cin hanci, da kuma tsoma baki ga harkokin irin na shari'ar a kasar da dai sauran su, inda suka ce suna da kwararan hujjoji da shaidu kan hakan. Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Somaliya, da na Tarayyar Afirka, da Tarayyar Turai, da ma kasashen Amerika da London, sun ja hankalin 'yan majalisar kan abun da ka iya biyo bayan tube shugaban kasar a wannan lokaci da ake fama matsalar tsaro.