Turai: Magance rikicin Ukraine da Rasha
September 4, 2025
Akwai dai fatan nan gaba Rasha da Ukraine za su cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a tsakaninsu, inda za su tura dakarun rundunar zuwa Ukraine ta kasance a kasa ko a teku ko kuma a sama. Shugabannin sun yanke wannan shawarar a karshen taron da suka kammala a Faransa, a kan yakin na Ukraine. Kusan dai ana yi wa wannan mataki na kasashen na Turai, kallon lisafin duna. Kasashen sun shirya bayar da tabbacin tsaro ga Ukraine, a ranar da aka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninta da Rasha. Shugaba Emmenuel Macron da yake magana a taron manema labarai jim kadan bayan taron ya ce, wannan rundunar ba ta da niyya ko manufa ta kaddamar da wani yaki a Rasha.
Ya kuma ce abin tambaya a yanzu shi ne, sahihancin alkawuran da Rasha ta dauka a lokacin da ta gabatar da shawarwarin zaman lafiya tare da Amurka. Shugabannin na kasahen Turai sun lashi takobin nuna wa Shugaba Vladimir Putin na Rasha cewa, ba za su saki Ukraine ba a cikin halin da take. Shugaban na Ukraine Vlodimir Zelensky bayan ya yi godiyya ga kasashen na Turai da Amurka, ya bayyana damuwarsa a kan matsayin Rasha na yin fatali da shirin tattaunawar. Jamus da Poland da Italiya da sauran kasahen Turai, sun yi alkawarin bayar da gudunmawa wajen kafa rundunar tsaron da za ta tabbatar da zaman lafiya in an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Rasha da Ukraine.