Kokarin warware rikicin Gabas ta Tsakiya
August 4, 2015![Symbolbild IS Soldaten](https://static.dw.com/image/18332689_800.webp)
Talla
Kamfanin dillancin labaran Iran na IRNA ya ce mukaddashin ministan harkokin wajen Rasha Mikhail Bogdanov da kuma mataimakin ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir-Abdollahian ma dai za su hallarci tattaunawar da za a yi.
Yayin zaman da za su yi dai, ana sa ran za wakilan kasashen uku su yi kokarin shata hanyoyin da za a bi na samar da zaman lafiya a Siriya da Yemen da kuma wasu kasashen da ke fama tashin hankali a yankin gabas ta tsakiya.