Kokarin warware rikicin Siriya
February 27, 2017Al-Hariri yabayyana hakan ne ga manema labarai jim kadan bayan tattaunawar da suka yi da babban jakadan Majalisar Dinkin Duniya a Siriyan Staffan de Mistura a birnin na Geneva, inda ya ce suna fatan tattaunawarsu da mahukuntan Rasha ta taimaka wajen sanya wakilan gwamnatin Siriyan su shiga cikin tattaunawa domin warware rikicin kasar ta hanyar kafa gwamnatin rikon kwarya. A hannu guda kuma 'yan adawar na Siriya sun zargi Moscow da saba tanade-tanaden yarjejeniyar tsagaita wuta a Siriyan sakamakon sabon harin da jiragen yakin da ake zargin na gwamnati ne ko kuma na Rashan suka kai a birnin Idlib. Koda a ranar Jumma'ar makon da ya gabata ma dai an kai wani harin kunar bakin wake a kasar ta Siriya, a dai-dai lokacin da aka fara tattaunawar ta Geneva karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya.