Halitta da Muhalli
Kokowa da kalubalen sauyin yanayi a duniya
November 17, 2016![Umweltprojekt-Trinkwasser aus Nebel in Marokko](https://static.dw.com/image/36401235_800.webp)
Talla
Taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi na COP22 na birnin Marrakesh na Maroko na a matsayin wata amsa ga sabon shugaban Amirka Donald Trump wanda a lokacin yakin neman zabensa ya bayyana adawarsa da yarjejeniyar COP21 ta birnin Paris. A daidai lokacin da kasashen duniya ke wannan taro tashar DW ta gabatar da rahotanni kan yadda matsalar sauyin yanayi ta kasance a wasu kasashen nahiyar Afirka.