1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koma baya ga matakan sojojin Masar

June 26, 2012

Kotun ƙoli a Masar ta yi watsi da dokar da ta ba wa sojoji yin aikin 'yan sanda, na tsarewa da gurfanar da masu laifi gaban kuliya.

Field Marshal Mohamed Hussein Tantawi, head of Egypt's ruling military council, points to a painting as he accompanies Turkish Prime Minister Recep Tayyip Erdogan, not pictured, at the defence ministry in Cairo, Egypt, Tuesday, Sept. 13, 2011. Erdogan, intent on broadening Turkey's influence in the Middle East and the Arab world, started a visit to Egypt and will also visit Tunisia and Libya, two other countries where popular uprisings have ousted autocratic leaders. (AP Photo/Amr Nabil, Pool)
Hoto: AP

Sai dai kotun ta ɗaga yanke hukunci kan halaccin rusa majalisar dokoki da kotun tsarin mulki ta yi zuwa ranar bakwai ga watan Yuli.

Dokar da kotun ta yi watsi da ita a ranar Talata, wacce sojoji suka shimfiɗa ta mako ɗaya bayan soke dokar ta ɓaci a ƙasar, na ɗaya daga cikin dokokin da masu fafutuka a ƙasar ke cewa, wata dabara ce ta sake wa dokar ta ɓacin da aka soke riga. Kuma ƙara bawa sojoji damar yiwa fararen hula hukunci ne a kotunan soji, lamarin da zai yi lahani ga jaririyar demokraɗiyyar ƙasar.

Wannan hukunci na zuwa ne a yayin da ɗaruruwan mutane ke shiga kwana na bakwai da fara yin zaman dirshan a dandalin Tahrir don tilasta wa mahukuntan sojin ƙasar dawo da rusasshiyar majalisar dokokin da sojoji suka rusata baki ɗaya, duk da cewa kotun tsarin mulkin ƙasar cewa ta yi a rusa ɗaya bisa uku na wakilanta kamar yadda masu fafutukar ke yin kira ga kotu da ta yi watsi da dokokin da mahukuntan soji suka shigar cikin kundin tsarin mulkin ƙasar, waɗanda suka basu ikon zartawa, sama da na shugaban ƙasa, ƙarar da ita ma kotun ta ɗaga yanke hukunci kanta zuwa ran 10 ga wata mai zuwa.

Sabon shugaba Masar na samun goyon bayan al'uma

"Muna so Muhammad Mursy ya yi aikinsa ba tare da anyi masa dabaibayi da wasu dokokin da akai haurensu cikin kundin tsarin mulki ba. Wannan kuwa ba zai taɓa yiwuwa ba,sai kowa ya tsaya a matsayinsa,kama daga yan sanda da masu shari'a gami da sojoji."

Daga yanke hukunci kan rusa majalisar dokoki har zuwa ran bakwai ga wata mai zuwa, na nufin sabon shugaban ƙasar Muhammad Mursy ba zai samu dammar yin rantsuwar kama aiki da zai yi ƙarshen wannan watan, a gaban majalisar dokokin ba kenan, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada. A maimakon hakan zai yi rantsuwar ne a gaban kotun ƙolin kasar,kamar yadda wata sabuwar dokar ko-ta-kwana da mahukuntan sojin kasar suka shigad da ita cikin kundin tsarin mulkin ta tsara don kaucewa wannan gibi da aka samu a ƙasar na rashin samuwar zaɓaɓɓiyar majalisar dokoki.

Hoto: Reuters

Batun yadda sabon shugaban ƙasar zai yi rantsuwar kama aiki na ci gaba da jawo taƙaddama tsakanin masana shari,a day an siyasa.A yayin da lauyoyin mahukunatan soji ke cewa,babu makaki kan shugaban yai rantsuwar kama aiki gaban kotun kolin kasar,tayin amfani da sabin dokokin da sojojin suka shigad da su cikin kundin tsarin mulkin kasar. Ita kuwa jam,iyar shugaban kasar ta Alhurriya Wal'adala, cewa tai,wannan mataki da mahukuntan sojin sukadauka wata gadar zare ce,da zata iya dasa alamar tambaya kan halaccin shugabancinsa,tun da bai yi rantsuwar tasa gaban majalisar dokoki ba.don haka,jam,iyar tace,tun da jami,an tsaro sun hana majalisar zama,tun bayan da sojoji suka rusasu,to yan majalisar za su haɗu a dandalin Tahrir don shugaban ya zo yai rantsuwar aiki gabansu.

Mawallafi: Mahmud Yaya Azare

Edita: Mohammad Nasiru Awal