Siyasar Chadi: Ci-gaba ko koma-baya?
December 17, 2025
Da ma dai al'ummar Chadin da dama ne ke yin tir da yanayin da ake ciki a kasar na tursasawa 'yan siyasa da 'yan fafutuka, tun bayan zaben Mahamat Idriss Déby Itno a watan Mayun shekara ta 2024 a matsayin shugaban kasa. A cikin wata sanarwa da suka fitar, kungiyar mabiya addinin Kirista sun bukaci shugaban Chadi da ya yi afuwa ga abokan hamayyar na siyasa.
Wadanne firsunonin siyasa ne a tsare?
Sunayen Succès Masra tsohon firaminista da Janar Idriss Youssouf Boy tsohon jam'in fadar shugaban, wadanda suke tsare a gidan yari watanni da dama ne dai, ke fita daga bakin al'umma kamar Malamin jami'a kana masanin kimiyyar siyasa Evariste Ngarlem Toldé: "Abin da kasa ke bukata kwanakin karshe na wannan shekara shi ne, sako fursunonin siyasa musammun ma Succes Masra da Idriss Youssouf Boy....."
Al'ummar Chadi na zargin gwamnatin da takaita 'yancin walwala na jama'a da siyasa da daure masu adawa da rashin kyakkyawan shugabanci da cin-hanci da rashawa da kuma yadda ake amfani da tsarin shari'a, wajen hukunta masu adawa da gwamnati.
Goyon baya daga masu rajin kare hakkin dan Adam
Shugaban Hukumar Kare Hakkin dan Adam, Belingar Laguerre ya yi kira ga manyan hukumomi, su dauki matakin kawo sassauci: "Yanayin Janar Idriss Youssouf Boy da Dakta Succès Masra ya kai matsayin da Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta Kasa (CNDH) ba ta adawa da sakinsu.......''
Mahamat Deby wanda ya dare kan karagar mulki bayan mutuwar mahaifinsa a 2020, an zabe shi a matsayin shugaban kasa na tsawon wa'adin shekaru bakwai da a kan iya sabuntawa har ba adadi, abin da 'yan adawar kasar suka kira koma-baya na dimukuradiyya.