Koma bayan yaki da cutar AIDS a Yuganda
July 23, 2014A yanzu dai Yuganda na fama da karancin kudi na yakar AIDS, musamman saboda kasashe da kungiyoyin duniya sun kaurace mata sakamakon manufofinta na nuna wariya ga masu neman jinsi guda a kasar.
Kasashe da kungiyoyin duniya sun rika zuba jari na kudi dubban miliyoyi a batun yaki da cutar AIDS a Yuganda, har zuwa lokacin da shi kansa wannan fanni matsalar cin rashawa da ta zama ruwan dare a kasar ta kawo kansa. Tsakanin shekara ta 2005 zuwa 2007, dollar miliyoyi dubbai ne suka bace, tare da zaton sun fada aljihun ma'aikatan hukumar lafiya ta kasar Yuganda ne. Tun daga wannan lokaci kasashen da kungiyoyin duniya suke janye jikinsu a game da baiwa kasar ta Yuganda taimakon kudi. Hakan ya sanya tun daga wannan lokaci aka kasa samun wani ci gaba a yaki da cutar Aids a kasar.
Annobar farko ta cutar AIDS a Yuganda ta barke ne a wani kauye na masunta mai suna Kasensero a yammacin kasar, inda ma a nan ne aka fara samun barkewar cutar a duniya baki daya, ko da shike wannan cuta an san ta nan da can a kasashen Tanzaniya da Kwango ko a Amrika, amma samun mace-mace da yawa tattare da wannan cuta ya zama sabon abu a wannan lokaci. Sanannen mai bincken cutuka na Yuganda, Joseph Kone-Lule, Prof a cibiyar bincike a asibitin hukuma dake birnin Kampala, yana daga cikin likitocin farko da suka fara bincike kan wannan annoba ta AIDS a shekara ta 1982. Yace tun da farko ya kwatanta cutar a matsayin barazana ga nahiyar Afirka. Yace:
"Gano yadda cutar take shine matakin farko mafi muhimmanci. Mun fara gudanar da binciken farko ne a shekara ta 1989, inda a yanzu muka lura da cewar wannan bincike ne na dogon lokaci. A ko wane shekaru biyar mukan maida hankalinmu kan wani fannin dabam. Wannan ma shi ya sanya ko wane lokaci ake samun canji a tsarin yaki da cutar ta AIDS. Da farko mun maida hankalinmu ne ga rukunin wadanda cutar tafi yiwa illa. Shin ta yaya mutum yakan kamu da kwayoyin cutar HIV, kuma ta yaya mutum yakan kamu da cutar AIDS? A yau mun fi maida hankali ne ga hanyoyin hana kamuwa da cutar. Muna da magunguna da mukan kyautata su ko wane lokaci, misali yadda za'a rage illolin da suke yi ga masu amfani dasu. Muna bincike kan hanyoyin hanyoyin da suka fi dacewa na warkar da cutar, ko da shike har yanzu muna nesa da samun nasarar hakan".
Yuganda ta dade a matsayin kasa ta misai kan batun yaki da cutar AIDS. Ma'aikatar kiwon lafiya, a sakamakon bincike, ta sami nasarar rage yaduwar cutar a shekaru na 90, idan aka kwatanta da sauran kasashen Afirka. A wancan lokaci Yuganda ta zama yar lelen kasashe da kungiyoyi masu bada agaji. Amirka da asusun kasa da kasa na yaki da AIDS sun rika baiwa Yuganda taimakon dollar miliyoyi dubbai. Cikin hakan ne a shekara ta 2003 adadin dollar miliyan 40 ya bace daga asusun yaki da cutar ta AIDS. Wannan kudi kuwa ba a gano inda yake ba sai a baya-bayan nan, sakamakon binciken kotuna da na wani dan jarida mai suna Edward Sekeywa. Yace Yuganda tana daya daga cikin kasashen da suka fi fama da matsalar cin rashawa a duniya.
"Dubi wadannan jerin gidajen. Wannan gidan shine cibiyar yaki da AIDS take amfani dashi, amma a zahiri gida ne mallakar tsohon ministan kiwon lafiya, wanda aka danka masa kudaden ciyar yaki da AIDS, wanda a hakika kudade ne na marasa lafiya da masu fma da AIDS, domin a saya masu magunguna, amma ya kwashe yayi yadda yake so dashi. Ya gina gidaje, ya sayi motoci. Wannan gidan ma ya bayar dashi haya ne ga Majalisar Dinkin Duniya, shi kuma yana zaune a wani gidan dake kusa.
Binciken baya-bayan nan ya nuna cewar matasa da masu matsakaicin karfi suna rage amfani da hanyoyin kariya daga cutar AIDS, misali amfan ida kwaroron roba yayin da basu tsaya kan abokiyar zama ko abokin zama daya ba. Hakan ya sanya tilas a sake sabon salo na matakin jan hankalin irin wannan rukuni domin fadakar dasu illolin dake tattare da cutar ta AIDS.
Mawallafi: Simone Schlindwein/Umaru Aliyu
Edita: Zainab Usman Shehu Usman